Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Gurfanar Da Mutum 65 A Gaban Kotu

0
676
Gwamna Malam Nasiru El-Rufa\'i na Jihar Kaduna

Rabo Haladu Daga Kaduna

GWAMNATIN JiharKaduna ta gurfanar da nutum 65 gaban kotu bisa zarginsu da hannu wajen haddasa rikici a Kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru ranar 26 ga watan
Fabarairun jiya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 12 tare da asarar dukiya mai tarin yawa.
Mataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Kaduna kan harkokin yada labarai Samuel Aruwan ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai, inda ya ce kotun ta dage sauraron karar har zuwa ranar 15 ga watan Maris din nan da muke ciki.
Samuel Aruwan ya bayyana cewa gwamnatin ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an hukunta duk wadanda aka samu da hannu cikin tayar da hankalin al’umma a Jihar ta Kaduna, sannan kuma ya bukaci al’ummar su rika mutunta juna.
Hakazalika ya yi kira ga jama’ar Jihar su kaucewa biyewa masu ingiza tashin hankalin addini ko kabilanci, ko ma wani tunzuri makamancinsa, kasancewar kundin tsarin mulkin kasar nan ya bai wa ko wane dankasa ‘yan-cin zama a ko ina tare da yin addinin da ya
ga dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here