Daga Usman Nasidi
RUNDUNAR a’yan sandan Jihar Ogun ta tasa keyar wani tsoho mai shekaru 70, Muyideen Alani gaban wata Kotun majistare da ke garin Ota na Jihar Ogun kan zarginsa da laifin kisan kai.
A zaman Kotu na ranar Litinin 12 ga watan Maris, Dan Sanda mai kara, Insifekta Abdulkareem Mustapha ya shaida wa Kotu cewa suna tuhumar Alani ne da laifin tukin ganganci, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Mohammed Lawan.
Majiyarmu ta samu labarin cewa Dan sandan yana fadin Alani ya tafka wannan aika aika ne a ranar 27 ga watan Fabrairu da misalin karfe 8:10 na safiyar ranar a tashar Mota ta Tempo, da ke Unguwar gonar Obasanjo, a Otta.
Dan sandan ya ci gaba da fadin; “Direban ya yi tukin ganganci ne a yayin da yake tuka wata motar Tipper ta dakon yashi mai lamba KTU 703 XV a kan hanyar, inda ya bankade Muhammed Lawan, sa’annan ya tattake shi.”
Majiyarmu ta ruwaito cewa Dan sandan ya ce laifin da ake tuhumar Alani ya ci karo da sashi na 5 da na 13 (1) na kundin dokokin manyan hanyoyin Jihar Ogun, na shekarar 2006.
Sai dai wanda ake tuhumar ya musanta tuhume-tuhumen, daga bisani bayan sauraron dukkanin bangarorin guda biyu sai Alkali Mathew Akinyemi ya bada belin wanda ake tuhumar a kan kudi N500,000.
Hakazalika Alkalin ya bukaci wanda ake tuhumar ya samo mutane guda biyu da za su tsaya masa, wadanda ke zama a yankin da Kotun ke zamanta, daga nan kuma ya dage sauraron karar zuwa ranar 3 ga watan Mayu.