Rabo Haladu Daga Kaduna
KIMANIN mutane 25 ne suka rasu, wasu kuma suka sami raunuka a wani hari da ake kyautata zaton na ramuwar gayya ne a karamar hukumar Kauru ta Kudancin Jihar Kaduna.
Rahotanni na nuna cewa an kai harin ne sanadiyyar wani rikici tsakanin al\’ummun karamar hukumar Bassa ta Jihar Filato da kuma na karamar hukumar Kauru da ke Jihar Kaduna.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce kimanin mutum 25 ne suka mutu a harin, sai dai duk da cewa hukumomi sun tabbatar da asarar rayuka, ba su fadi adadin wadanda suka mutu ba.Amma gwamnatin jihar Kaduna ta ce ta umarci jami\’an tsaro da su tsaurara tsaro a iyakar Jihar Filato da Kaduna don gudun sake afkuwar wani harin.
Haka kuma a wata sanarwa da ta fitar, gwamnatin Kadunan ta bukaci gwamnatin jihar
Filato da ta taimaka wajen farauto wadanda suka kai harin suka kuma halaka \’yan jihar ta Kaduna.
A baya-bayan nan dai ana yawan samun tashe-tahsen hankula tsakanin wasu kabilu daban-daban a jihar Kaduna, al\’amarin da ke jawo asarar rayuka da dukiyoyi.
Gwamnatin jihar ta sha shan alwashin sanya kafar wando daya da masu haddasa tashin hankali a jihar sai dai ga alama har yanzu ana ci gaba da samun tashe-tashen hankula nan da can.