Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABAN kasa zai kaddamar da wani katafaren kamfanin sarafa sikari a Jihar Neja wanda ya lakume kudi Naira Miliyan Dubu 50, zai ba mutane kimanin dubu 10 aiki da bunkasa noman rake a yankin da ma kewaye.
Kamfanin mai suna Sunti an yi shi ne a garin Kusogi da ke cikin karamar hukumar Mokwa a jihar Neja.
Mataimakin gwamnan jihar Neja Alhaji Ahmad Muhammad Gyetso wanda shi ne shugaban kwamitin tarbar shugaban kasa, ya tabbatar da kammala duk wani shiri na karbar Shugaba Buhari.
Alhaji Gyetso ya nemi hadin kan jama\’a domin a gama bikin bude kamfanin lafiya.
Kazalika babbar jam\’iyyar adawa, PDP ta bakin shugabanta na reshen jihar, Barrister Tanko Beji inji shi, zuwan shugaban kasa jihar alheri ne gare su. Ya ce shugaban zai kaddamar da kamfanin da \’yan kasuwa masu zaman kansu suka gina abin da zai habaka tattalin arzikinsu. Ya yi fatan Allah ya kawo shugaban lafiya ya kuma mayar da shi gida lafiya.
Rundunar \’yan sandan jihar ta ce ta kara jami\’an tsaro a wurin da za a kaddamar da bikin.