Mustapha Imrana Abdullahi
RUNDUNAR \’yan sandan tarayyar Nijeriya shiyyar Jihar Sakkwato ta bayyana nasarar kame wani mutum da ya ce ya fito ne daga garin Domin Dutse a Jamhuriyar Nijar.
Kwamishinan \’yan sanda Malam Muktar ya shaidawa manema labarai ta bakin mai magana da yawun rundunar cewa sun yi nasarar kame wannan mutum ne dauke da makamai da ya tabbatar masu cewa yana farauta ne Kuma shi ne shugaban \’yan farautar Dogon Dutse da ke kasar Nijar.
\”Amma mun same shi da bindigu a tare da shi babbar bindigar tana dauke da harsashi sama da saba\’in sai kuma karamar mai dauke da harsasai guda shida, an kuma sane shi da kakin soja da bel da sauran kayayyaki\”.
\”Don haka mu ba mu son ganinsa ko wasu mutane irinsa a jiharmu baki daya\”
Babban abin la\’akari a nan shi ne ya dace mutane su tashi tsaye wajen aikin sa idanu ga dukkan wani abu da ba su gane masa ba su gaya wa jami\’an tsaro domin daukar mataki doka kamar yadda ya dace.