KARAR KWANA: WANI MATASHI YA HALLAKA KANSA GARIN SATA A TIRANSIFOMA 

0
689

Daga Usman Nasidi

JAMA\’A na cewa duk wanda ya biye ma ransa ya yi abin da take so, tabbas zai ga abin da ba ya so kuwa, wanda kwatankwacin haka ne ta faru da wani matashi a Jihar Kaduna mai budurwar zuciya.

Wannan lamari ya faru ne a unguwar Barnawa High cost da ke cikin garin Kaduna, inda aka wayi gari aka tsinci gawar wani matashi a makale da na’urar rarraba wutar lantarki, wato tiransifoma.

Majiyarmu ta samu labarin cewa jama’ar unguwar na cewa suna zargin mutumin barawo ne, kuma ya yi kokarin sace musu Tiransifoma ne, ko kuma wani abu daga cikin Tiransifomar, da ake sacewa ake siyawar.

Kamar yadda aka ga gawar mutumin, ta nuna cewar hawa ya yi kan wasu manyan falwayoyin wuta guda biyu, wadanda suke dauke da na’urar tiransifomar a can sama, inda barawon ya dare da nufin kwantota.

Daga bisani a safiyar Juma’a, an hangi jami’an hukumar wutar lantarki ta Kaduna, KAEDCO, sun isa wajen, inda suka bambabaro gawar barawon daga jikin karafan da ya makale da su a saman.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here