0
1240
I G Na \'Yan Sandan Najeriya

Ba Za Mu Ba Wa Buhari Kunya Ba –Shafiu Ahmed

Rabo Haladu Daga Kaduna

Kamfanin Samar da taki na ‘ CITIZEN FERTILIZER AND CHEMICALS’ yana daya daga cikin kamfanonin da gwamnatin tarayya ta sanya a cikin shirin na samar da taki ga manoma, wanda shi ma a wannan shekarar ya shiga cikin sahun sauran kamfanonin sarrafa takin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kamfanin shi ne kan gaba wajen samar da takin zamani a Arewacin kasar sama da shekaru 15 da suka gabata. Hakan ya sanya kungiyar masu samar da taki ta kasa (FEPSAN) ta sanya kamfanin a cikin shirin.
A wata zantawa ta musamma da yayi da manema labarai a Kano, shugaban kamfanin sarrafa takin da ke Jihar Kano, Alhaji Shafi’u Ahmed, ya bayyana cewa kamfaninsu ya shiryya tsaf wajen bayar da tasa gudummawar domin ganin an ci gaba da samar da taki mai inganci.
A kan hakan, shugaban ya bayyana cewa kamfanin su ya tanadi kayan aiki irin na zamani domin ganin an Samar da taki me kyau kuma cikin lokaci.
Ya ce, sun cika duk ka’idojin da ake bukata na shiga cikin tsarin samar da takin gwamnatin. Idan ba’a manta ba,gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta
kulla yarjejeniya da kasar Moroko, da kuma kungiyar masu sarrafa taki ta Nijeriya da nufin ganin an samar da dukkan sinadaran da ake bukata domin hada takin cikin farashi mai sauki domin sayar da shi ga manoma a cikin sauki.
A wata ganawa da wakilinmu kwanan baya, Mista Thomas Echo, wanda shi ne shugaban kungiyar masu sarrafa taki ta Nijeriya ( FEPSAN) wadda aka hada
wannan yarjejeniya da shi, ya bayyana cewa an kulla yarjejeniyar ne kan cewa kungiyar ta samowa manoma taki mai rahusa.
Shugaban kungiyar ya kara da cewa buhun takin da ake sayarwa Naira Dubu goma, wannan sabon shiri na bayar da takin a kan kudi Naira Dubu biyar da dari biyar ne kacal. Kuma takin zai kai ga manoma ne ta hanyar gwamnatocin jihohi da dillalai da sauran ‘yan kasuwa, wadanda kamfanin ke basu a kan farashin kowane buhu a kan kudi Naira Dubu biyar su kuma su kara naira dari 500.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here