Janyewar Dam Na Gwaranyo:  Mutane Akalla Miliyan Hudu Na Cikin Hadarin Rashin Ruwa Abokin Aiki – Tambuwal

0
660
Gwamna Aminu Waziri Tambuwal Na Jihar Sakkwato dan takarar shugaban kasa a jam\'iyyar PDP

Rahoton Zubair Sada Da Mustapha Imrana Abdullahi

GWAMNAN Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya shawarci masu ruwa da tsaki a kan batun inganta madatsar ruwan Gwaranyo domin ceton shi daga halin kafewar da yake ciki

Bayanin da ke fitowa a game da dam din na nuni da cewa dam din ya kafe da kashi casa\’in cikin dari.

Mutanen wajen na amfani da dam din a matsayin hanyar samun ruwa ga mutane Miliyan hudu da suke a Jihohin Sakkwato da Kebbi a yankin  Arewa maso Yammacin Nijeriya., suna yin amfani da shi domin yin noman rani da kuma amfanin yau da kullum a jihohin biyu.

Da yake jawabi lokacin da ya ziyarci wurin dam din, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya ce hakika halin da madatsar ruwan ke ciki abin bakin ciki ne kwarai da ke haifar da fargaba.

\”An Gina madatsar ruwan ne domin ta ajiye ruwan da ya kai yawan biliyan daya, amma a halin da wurin yake ciki ruwan da ke cikin dam din bai wuce yawan miliyan dari ba\”.Wanda hakan ya haifar da matsalar karancin ruwa ga hukumar samar da ruwa wanda hakan ke haifar da matsalar bayar da ruwan ga mutane\”.inji Gwamnan.

Tambuwal ya ci gaba da cewa, \”Haka kuma manomanmu na cikin matsalar ruwa musamman ga manoman rani. Don haka muna shwartar masu ruwa da tsaki musamman gwamnatin tarayya, domin wucewa gaba ta yadda za a ceto wannan madatsar ruwa musamman idan aka yi la’akari da irin mutanen da ke amfana da dam din don gudanar da rayuwasu ta yau da kullum, janyewar ruwan ya haifar da nakasu ga harkar samunsu\”. Inji Tambuwal.

Da yake zagayawa da Gwamnan domin ganin halin da dam din yake ciki, Manajan Daraktan hukumar kula da Dam din na Sakkawato-Rima Injiniya Buhari Bature, ya ce kafewar dam din na yanzu ya fi na kowace shekara lalacewa na tsawon shekaru ashirin da biyar.

Ya kuma danganta matsalar karancin ruwan da irin yadda aka samu karancin ruwan sama a shekarar 2017 da ta gabata sakamakon matsalar canjin yanayi.

Ya kuma tabbatar da matsalar ta shafi ayyukan hukumar samar da ruwa ta jihar da kuma manoman rani na jihohin Sakkwato da Kebbi

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here