Muhammad Sani Chinade, Daga Damaturu
A ziyarar jajantawa da ya kai a garin Dapchi cikin karamar hukumar
Bursari a Jihar Yobe Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada tabbaci ga
iyalen \’yan matan makarantar sakandaren kimiyya da fasaha dake garin
na Dapchi wadanda \’yan kungiyar Boko Haram suka sace musu yara kusan
kimanin 110 yau kusan kimanin makonni uku da suka shude cewar, a
shirye ya ke da ya ga an kwato wadannan yara ko ana ha maza ha mata
cikin kankanin lokacin dake tafe.
Shugaba Muhammadu Buhari a ganawar ta sa da iyalen \’yan mata kimanin
110 da \’yan kungiyar ta Boko Haram suka sace kasa da makonni 4 da suka
gabata a makarantar ta sakandaren GGSTC da ke garin na Dapchi ya
tabbatar musu cewar tunin jami\’an tsaron kasar nan na sama da na kasa
sun dukufa ka\’in da na\’in don ganin sun kwato wadannan yaran.
Daga sai shugaban ya bada hakuri ga iyayen dangane da wannan irin
iftila\’i da ya fada musu na sace yaransu. Tare da cewar irin matakan
da gwamnatinsa ke dauka dangane da kwato wadannan \’yan mata cikin
lokaci sabanin gwamnatin da ta shude karkashin tsohon shugaban kasa
Jonathan da aka sace \’yan matan Chibok da suka rika jan kafa wajen
ceto su.
Da yake jawabi a madadin iyayen yaran da aka sace, shugaban kungiyar
iyayen Alhaji Bashir Manzo godiyarsu ya nuna ga shugaban kasa
Muhammadu Buhari dangane da wannan ziyara ta jajantawa da ya kawo musu
gari da gari har zuwa garin na Dapchi wadda a cewarsa hakan ya nuna
cewar lalle shugaban ya damu da wannan lamari.
Ya kuma kara jaddada bukatarsu ga shugaban kasar na ko ta halin kaka a
taimaka don ceto musu \’ya\’yansu ko a raye ko a mace, a cewarsa yin
hakan ne zai ba su nutsuwa da kwanciyar hankali.
Tun farko kafin shugaban kasar ya kai ziyara garin na Dapchi sai da ya
gana da gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahhm Gaidam a gidan gwamnatin
dake garin Damaturu inda ya jajanta masa kan wannan lamari tare da ba
shi tabbacin cewar, ta ko halin kaka jami\’an tsaro na hobbasan ganin
sun gano wadannan dalibai. Kana shi kuma Gwamnan ya gode wa shugaban
kasar dangane wannan ziyarar jajantawa da ya kawo musu tare da ba shi
tabbacin hada gwiwa da gwamnatin Jihar ta Yobe don ganin an kai ga
nasarar ceto wadannan \’yan makaranta.