Wasu Gungun Matasa Sun Gudanar Da Zanga-zangar Lumana A Yobe Kan Tursasawar \’Yan Sintiri

0
693
Gwamna Gaidam: Sha yabo katafila sarkin aiki

 

Muhammad Sani Chinade, Daga Damaturu
WASU gungun matasa a garin Ngelzarma cikin karamar hukumar Fune a
Jihar Yobe sun gudanar da zanga-zangar lumana zuwa kofar mai martaba
Sarkin Ngelzarma Alhaji Muhammad Zanna Mai Yeri 111 don nuna bacin
ransu dangane da yadda suke zargin kan cewar wasu mambobin kungiyar
\’yan sintiri dake garin sun je sun far musu ya yin da suke gudanar da
hidimar bikin wani abokinsu ba tare da sun wuce ka\’idar lokacin da
dokar hana walwala ta fara aiki ba.
Wani daga cikin matasan da abin ya shafa wanda ya nemi a boye sunansa
ya bayyanawa wakilinmu ta wayar tafi da gidanka cewar, su matasan sun
gudanar da wannan zanga-zangar lumana ne ya zuwa kofar mai martaba
Sarkin na Ngelzarma ne don nuna rashin jin dadinsu bisa ga aika-aikar
da wasu mambobin kungiyar \’yan sintirin suka musu a ranar lahdi da
daddare wajen misalin karfe 9.15 na dare, yayin da suke gudanar da bikin
abokinsu inda suka far musu da duka tare da shiga gidajen matan aure
dake kusa da wurin suna dukan kan mai uwa da wabi maza da mata, wannan
daliline ya kawo mu da zanga-zanga don nuna damuwar mu.
Malami ya kara da cewar, duk da zanga-zangar lumanar da suka gudanar
amma abin ban takaici mai martaba sarkin na Ngelzarma bai saurare su
ba maimakon hakan ma sai kawai aka turo mana sojoji suka tarwatsa mu
tare da bugun mu kamar kurar roko, daga bisani ma aka kame mana mutane
kimanin 5 aka tafi da su Damagum aka rufe su wadda hakan ke nunawa
tamfar ba mulkin dimukuradiyya ake ba.
Kan hakan ne wakilin mu ya nemi shugaban karamar hukumar Fune Alhaji
Dima Gana ta wayarsa ta tafi da gidanka kan ko yana sane da abin da ya
faru? Nan ya kada baki ya ce, lalle ya samu labarin hakan don har ma
ya je garin na Ngelzarma da kansa don tabbatar da lamarin to amma kuma
magana ta gaskiya matansa ne suka karya doka domin kowa ya san cewar,
a jihar Yobe  akwai dokar hana walwala daga karfe goma na dare 10.00pm
zuwa karfe 6.00 na safe, to matasan sun wuce wannan ka\’idar ne shi
ya sa \’yan sintirin suka tarwatsa su.
Don haka shi a iya sanin yaro daya ne dan gidan Alhaji Bello Tabaco
shi ya haddasa wannan lamari kuma dole ne a bi doka, babu kuma wanda
aka yi wa rotse illa dai \’yan sintirin sun tarwatsa matasan ne da
zimmar kora su gidajensu kasancewar sun zarta lokacin doka na karfe
10.00 na dare.
Kan wannan lamari wakilinmu ya samu ganawa da sakaren mai martaba
Sarkin na Ngelzarma Alhaji Suleman Zanna yadda ya bayyana cewar lalle
matasan sun zo kofar mai martaba amma kuma da aka ce musu su zabo
mutane 5 daga cikinsu don ganawa da su tare da jin koken su a madadin
sauran, anan sai suka rika ihu cikin hakan ne sai ga sojoji sun iso
fadar cikin motarsu shi ne ganin haka matasan suka tarwatse. Wannan
shi ne abin da ya faru.
Sakataren ya kara da cewar a yanzu haka kuma mai martaba Sarki ya sa
an kira masa wasu matasan don tattaunawa da su don samo bakin zaren
magance sake faruwar hakan tun Jihar Yobe Jiha ce da ke cikin
takaitaccen lokacin walwala daga karfe 10.00pm zuwa karfe 6.00am na
safiyar kowace rana a dukannin fadin Jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here