Rabo Haladu Daga Kaduna
RAHOTANNIN da muke samu sun ce mayakan Boko Haram sun sako \’yan matan Dapchi da aka sace a watan jiya.
Daya daga cikin iyayen yaran ya shaida wa manema labarai cewa da sanyin safiyar ranar Laraba ne wasu mutane suka mayar da yaran garin a motoci. Inda suka a jiye su suka yi tafiyarsu.
Ya kara da cewa iyaye na ta rububin zuwa domin dubawa da kuma dauko \’ya\’yansu.