Janyewar Dam Na Gwaranyo: Hukuncin Allah Ne Don Jarrabawar BayinSa

0
702
Mulkin Gwamna Aminu Tambuwal na tallafa wa rayukan al\'umma baki daya

Daga Zubair Abdullahi Sada

GWAMNAN Jihar Sakkwato, Rt Hon. Aminu Waziri Tambuwal ya ce, janyewa ko kafewar Dam na Gwaranyo nufin Allah ne tare da hukuncinSa wanda babu wani abin halitta da zai iya hana afkuwar hakan, sai dai mutane su ci gaba da addu’o’i na neman gafarar Allah da kwaranyewar wannan musifa.

Gwamnan yana wannan batu ne cikin batutuwan da ya gabatar a yayin da ya kai ziyara Dam din na Gwaranyo wanda kafewarsa ta janyo karancin ruwa a Sakkwato da wasu sassan Jihar Kebbi. Ya ce, su a gwamnatance sun tabbatar kafewar Dam din ya faru ne dalilin karancin ruwan sama da aka samu a daminar bara, don haka ne duk mai imani ya san al’amarin nufi ne kaddara ce daga Mahaliccin kowa da komai.

Sai Gwamnan ya ce, su a bangarorin gwamnati da suke da alhakin samar da ruwa tsaftatacce ba su fasa bai wa hukumar ruwan kudaden sayo magunguna da sauran abubuwan da ma’adinan ke bukata ba. Inda ya fada cewa, akalla kowane wata gwamnatinsa na kebe kusan Naira Miliyan 170 ga hukumar.

‘’Muna kira da babbar murya tare da rokon gwamnatin tarayya da ta dube mu da idon rahama ta agaza mana domin samar da Dam din nan ya fara aiki, domin rashin aikinsa zai sanya kusan kimanin mutane Miliyan hudu cikin halin-ni-‘ya su’’. Inji Gwamna Tambuwal.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here