GWAMNA EL-RUFAI YA SANYA TUBALIN GINA GIDAJE 600 MASU RAHUSA A GARIN KADUNA

0
644
Daga Usman Nasidi
GWAMNAN jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya kaddamar da fara ginin wasu gidaje guda 600 a jihar Kaduna masu rangwame, inda ya sanya tubalin ginin a ranar Laraba 21 ga watan Maris.
An gudanar da taron sanya tubalin gidajen ne a unguwar Millenium City na jihar Kaduna, gine-ginen da suka kunshi gidaje 600, da katafaren shagon siyayya.
Majiyarmu ta samu labarin cewa za a yi wannan gine-gine ne da hadin gwiwa tsakanin hukumar bunkasa kasuwanci ta jihar Kaduna, KADIPA da kuma wasu kamfanonin \’yan kasuwa da suka hada da Nurus-Siraj da za su gina gidaje 500, Ummhi Nigeria masu gidaje 100, sai kuma, Kamfanin Jifatu.
A yayin taron Gwamna El-Rufai ya bayyana cewar gwamnatin jihar za ta samar da ruwan famfo, wutar lantarki da kuma tsaro a unguwannin da ake gina gidajen, sa’annan ya bukaci jama’an unguwannin da su bai wa kamfanonin hadin kai don a yi aiki tare da su.
“Ina fatar za mu dawo nan da shekara daya don kaddamar da kammala ginin gidajen nan, dama an sanar da mu cewar za a kammala gina katafaren shagon nan a watan Yuni.” Inji El-Rufai.
Da take nata jawabin, shugaban hukumar KADIPA, Umma Aboki ta bayyana cewa a gwamnati na da yakinin kamfanoni masu gine-gine za su samar da gidajen da suka kai 3000 a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Hakazalika ta tabbatar da manufar KADIPA na hada karfi da karfe da \’yan kasuwa don inganta kasuwanci a jihar Kaduna ta hanyar samar da shagunan zamani akan tsari, tare da samar musu da yanayi mai kyau don bunkasa kasuwancinsu.
Bugu da kari bayan wannan bikin sanya tubali, Gwamnan ya kara halartar taron sanya tubalin gina Otal da wajen shakatawa a bayan dandalin Murtala da ke cikin garin Kaduna, wanda kamfanin AMSALCO ke ginawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here