Daga Usman Nasidi
AKALLA sojoji 11 ne suka rasa rayyukansu sakamakon artabun da aka yi da \’yan bindigar, wasu kuma sun jikkata wanda hakan ya sanaya Hukumar Soji da Gwamnatin jihar Kaduna suka ce za su yi bayyani kan lamarin bayan sun gama kamalla bincikensu.
Rahotanni sun bayyana cewa sojoji guda 11 ne suka rasa rayyukansu a wani hari da wasu \’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka kai a sansanin sojoji da ke garin Kamfanin Doka a hanyar Funtuwa da ke karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna.
Sojoji 11 sun mutu yayin da \’yan bindiga suka kai hari a sansanin sojin inda wakilinmu ya tabbatar da cewa harin ya faru a daren jiya Talata.
Hakazalika, wani tsohon shugaban karamar hukuma da ya nemi a sakaya sunnan sa saboda ba shi da izinin tsokaci kan lamarin ya tabbatar da faruwar harin.
Ya kara da cewa bayan wandanda suka rasu, wasu sojojin uku da kuma wasu \’yan banga sun sami raunnuka.
\’Yan bindigan sun kai hari ne a sansanin sojojin da ke Kamfanin Doka a hanyar Funtua. Sojoji 11 sun rasa rayyukansu kuma wasu 3 sun jikata.
\’Yan bindigan har ila yau sun kai farmaki ga yan banga a Maganga, wani gari da ke kilomita 44 daga Birnin Gwari a safiyar Laraba a yayin da suka je taimakawa sojojin. Guda tara sun sami raunuka, an garzaya da su asibiti a halin yanzu, \” inji shi.
Ya yi bayannin cewa yan bindigan sun iso ne a kan babur misalin karfe 10,05 na dare a daren Talata inda suka yi ta artabu da sojojin.
Yayin da aka tuntubi jam\’in hulda da jama\’a na One Mechanised Division, Mohammed Dole, ya ce: \” A halin yanzu muna cikin daji don tattara bayanai kan abin da ya faru. Za mu fitar da sanarwa bayan mun kammala bincike, a kara hakuri .\”
Hakazalika, mai magana da yawun Gwamnan Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce gwamnati za ta yi tsokaci kan lamarin idan sun sami bayanai.