Ba Zan Amince Da Abin Da Ba Zai Amfani Nijeriya Ba – Buhari

0
832
Shugaba Buhari a wata ziyrar aik a Filato
  Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
SHUGABAN kasar tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewa babban dalilinsa na dakatar da zuwansa kasar Ruwanda wajen taron batun kasuwanci shi ne domin ya kara nazartar irin yadda tanaje-tanajen yarjejeniyar da ake kokarin sanya wa hannu sosai.
Mai magana da yawun Muhammadu Buhari a game da batun yada labarai Mista Femi Adesina ya bayyana hakan. Inda ya ce hakika ba zai taba sanya wa duk wata yarjejeniyar da bai kammala nazartarta ba hannu, domin ya fi son kasarsa Nijeriya ta ci gaba.
\”Sai na fahimci irin yadda tsarin yake da kuma alfanun da Nijeriya za ta samu a fannin tattalin arzikin kasa da tsaro domin amfanin \’yan kasa baki daya\”.
Don haka ya zama wajibi ga jama\’a su fahimci cewa ba zan yi abin da zai ciyar da kasa ta Nijeriya baya ba.
A gefe daya kuma shugaban ya bayar da tabbacin cewa zai hukunta dukkan magoya bayan tsoho Buharin Daji.
\”Na bayar da umarni ga jami\’an tsaron DSS da su ci gaba da Samo bayanai a kan kungiyar Buharin Daji da dukkan magoya bayansa domin yin maganinsu da kungiyar baki daya\”. Inji Muhammadu Buhari na Nijeriya.

 

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here