CIBIYAR BINCIKE DA BADA MAGUNGUNA TA DANKOLO TA FADADA AIYUKANTA

    0
    860
    JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
    SHUGABAN cibiyar bincike da bada magunguna ta  \”Dankolo Traditional Pharmacy\”  da ke garin Dawanau kwanar Dawakin Tofa Dokta Laminu  Salisu Dogon Malam ya ce cibiyarsa ta fadada ayyukanta na bincike kan wasu nau\’in cututtuka wadanda kuma suke da bukatar samar da magunguna domin masu dauke da su.
    Ya yi wannan bayani ne  a wata ganawar su da wakilinmu, inda ya sanar da cewa cibiyar Dan Kolo ta himmatu wajen ganin an ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan wasu cututtuka ta yadda za a samo irin magungunan da ake bukata tare da ba da shawarwari ingantattu kuma masu amfani ga masu dauke da su.
    Sannan ya ce suna da kwararrun mutane da ke gudanar da cikakken bincike kan cututtuka masu barazana ga al\’uma, sannan suna da kwarewa wajen bayar da  magani bayan an tabbatar da nau\’in cutar da ke damun mutun domin ganin an sami dacewa a kodayaushe.
    Haka kuma Dokta Laminu Dogon Malam ya sanar da cewa sun dade suna aikin bincike da ba da magunguna,  kuma ana samun waraka bisa yardar Ubangiji, don haka ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga al\’uma da su rika tantance guraren da za su nemi magungunan gargajiya domin kauce wa abin nan da ake cewa cuta daban kuma magani daban.
    A karshe, ya jaddada cewa za su ci gaba da kokarin samar da ingantattun magunguna domin taimaka wa al\’uma bisa larurorin da ke addabar su,kuma babban ofishinsu yana nan a garin Dawanau kwanar Dawakin Tofa domin neman magani ko kuma shawarwari kan irin larurar da ke damun su.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here