Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
\’YAN kungiyar sintiri na sa kai da ake kira da sunan \’yan Karota sun yi nasarar kama wani kasurgumin barawon da ya dade yana sace-sacen da suka hadar da Babura a garin Funtuwa yana Kai wa wadansu wurare yana sayarwa
Shi dai wannan mutum da ya dade a kan wannan harkar haifar wa da dimbin jama\’a bakin ciki dubunsa ta cika ne lokacin da ya dauko wani mai sana\’ar daukar mutane a babura daga bakin Tashar motar Funtuwa da daddare inda ya bukaci ya Kai su unguwar Tudun Wada da ke cikin garin Funtuwa.
Amma da suka je kan hanya cikin Mangwarori a jefen unguwar Turawa da ake kira (GRA) sai ya ce wa mai tukasu ya bi ta hanyar jikin Gidan Talbijin na NTA kamar za su shiga Tudun wada, amma nan take kafin isa cikin unguwar sai barayin biyu suka yi kokarin kawar da mai rikon domin su gudu da Babur din.
Cikin hukuncin Allah daya daga cikin barayin ashe akwai bindiga a jikinsa sai ya fitar da ita amma taki tashi, sakamakon ihun neman daukin da direban Babur din ya rika yi nan da nan jama\’ar Annabi suka fito kuma kamar yadda kowa ya sani suka ce da wa Allah ya hada su ba da matukin Babur ba?
Ganin haka sai suka ranta a na kare wato kafa me na ci ban ba ki ba sai dai rashin sa\’a mai rike da bindigar ya fada wani gida domin ceton ransa daga jama\’a inda ya fada karkashin mota da ya shiga gidan ya kuma boye bindigar amma duk da haka asiri ya tonu nan take ya shiga hannun \’yan karotar unguwar.
Sun kuma tambaye shi inda ya samo wannan bindigar da kuma irin sace-sacen da ya taba yi?
Kuma nan take ya amsa masu da cewa a kasar Nijar ya sayo ta kuma da akwai wani Babur da aka taba sacewa na wani mutum mai sana\’ar tireda a nan Tudun Wada shi ya sace shi misalin shekaru biyu da suka gabata.
\’Yan karotan dai sun mika barayin biyu a hannun \’yan sanda kamar yadda dokar kasa ta tanadar.
Bayan sun bi wanda ya tsere sun kama shi suna kuma kokarin kama mutum na uku da barayin suka tabbatar masu da inda yake zama da lokacin da yakan je wajen.
Sai dai hakika \’yan kungiyar sintirin duk da irin namijin kokarin da suke yi suna bukatar masu hannu da shuni su rika taimaka masu domin samun kayan aiki musamman irin bayanan da muke samu na cewa rashin kudin abin hawa ya hana su zuwa kamo barawon na uku domin in sun kama shi babu kudin da za su dora shi a Babur su kai shi ofishin \’yan sanda.