0
1293
Gwamna Ganduje Na Jihar Kano

MUN GAMSU DA SALON MULKIN GWAMNA GANDUJE-MUSTAPHA  COACH.

 

 

Jabiru A Hassan,  Daga Kano.

 

 

JAGORAN matasan Kano ta Arewa Kwamared Mustapha Umar Tallo Gwarzo ya ce matasan Jihar Kano  suna gamsuwa da salon mulkin Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje musamman ganin yadda jihar take samun ci gaba ta kowane fanni duk da yanayin matsin tattalin arziki da ake ciki a halin yanzu.

Ya yi wannan bayani ne cikin tattaunawarsu da wakilinmu, inda ya nunar da cewa Gwamna Ganduje ya ciri tuta idan aka dubi irin ayyukan da gwamnatinsa ke yi a kowane lungu da sako na fadin jihar ba tare  da nuna bambancin siyasa ko na ra\’ayi ba.

Haka kuma jagoran matasan ya sanar da cewa duk wanda ya je Jihar Kano zai yarda cewa gwamnati mai ci tana kokari sosai wajen aiwatar da aikace-aikace masu inganci kuma bisa yin la\’akari da bukatun al\’uma, wanda a cewarsa hakan abin a yaba ne koda kuwa ana adawa da gwamnatin.

Kwamared Mustapha Umar Tallo Gwarzo ya bada misali ga yadda Gwamna Ganduje yake bunkasa rayuwar mata da matasa ta hanyoyi daban-daban, da kyautata yanayin harkar lafiya da inganta asibitoci manya da matsakaita da kuma kanana har ma da sanya kayan aiki domin kula da lafiyar al\’umar Jihar Kano.

Dangane da batun siyasar jihar kuwa, Mustapha Tallo Gwarzo ya ce an sami nasarori masu tarin yawa ta fannin kyautata siyasa da adawa mai ma\’ana domin kara yi wa gwamnati tuni kan abubuwan da al\’uma suke bukata ba tare da samun rashin jituwa ko tashin hankali ba, inda kuma ya jinjina wa shugabanni da jagororin jam\’iyyar APC mai mulki bisa tsaftace siyasar jihar da ake yi.

Sannan kuma ya yi godiya ga sabon zababben shugaban karamar hukumar Gwarzo Injiniya Bashir Abdullahi Kutama, saboda kokarin da yake yi wajen kawo  karshen matsalar ruwa a garin Gwarzo da sauran ayyuka na alheri a fadin karamar hukumar, wanda hakan ta sanya ake yi masa jinjina da fatan alheri tun da ya karbi ragamar mulkin karamar hukumar.

A karshe  jagoran matasan ya yi  kira ga daukacin al\’umar karamar hukumar ta  Gwarzo da su kara bai wa shugaban karamar hukumar goyon baya da hadin kai saboda kyawawan manufofin da yake da su na ciyar da yankin gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here