Jabiru Hassan, Daga Kano
WANI fitaccen mai sana\’ar sayar da gyada da ke Dawanau Malam Ali Sona, wanda aka fi sani da \” mai gyada don mata\” ya ce yana taimaka wa mata da bashin gyada ne domin su dogara da kansu a matsayin su na iyayen al\’uma.
Ya yi wannan bayani ne a ganawar su da wakilinmu, inda ya bayyana cewa ya shafe fiye da shekaru goma sha bakwai yana bai wa mata bashin gyada suna biya sannu a hankali domin taimaka masu wajen jin dadin zamantakewa saboda a cewarsa, mata su ne suke da bukatar taimako daga masu iko.
Malam Ali Sona ya kuma sanar da cewa ya zabi ya taimaka wa mata ne saboda su ne suke yawan shiga yanayi na tausayawa, sannan su ne ake yawan mutuwa ana barin su da yara kanana don haka yake taimaka masu da bashin gyada sai sun sarrafa sun sayar kana su biya shi domin su sami abin da za su dogara da kan su.
Bugu da kari, mai gyada don mata yana ba da bashin gyada ga mata koda bai san su ba, sannan ya ce tun da ya fara wannan sana\’a bai taba samun wata matsala ba a shekaru goma sha bakwai din da ya yi yana yi, kana dukkanin matan da yake bai wa gyada bashi ba sa wasa wajen maido masa da kudinsa idan sun sayar da abin da suka sarrafa.
Ya bayyana cewa ya fara wannan sana\’a da buhu biyu kacal, amma yanzu yana iya bada buhu hamsin ba tare da wata matsala ba, tare da yin kira ga masu karbar kaya da su ci gaba da kasancewa masu rikon amana da tsare gaskiya ta yadda al\’amura za su ci gaba da tafiya cikin nasara.
A karshe, Ali mai gyada don mata ya yi amfani da wannan dama wajen jaddada ci gaba da taimaka wa mata domin ganin rayuwarsu tana kara bunkasa, sannan ya jinjna wa Gwamnatin Jihar Kano da ma\’aikatar kula da al\’amuran mata ta jihar, saboda kokarin da take yi wajen samar da karin hanyoyi na taimaka wa mata ba tare da nuna gajiyawa ba.