Jabiru A Hassan, Daga Kano.
ZABABBEN shugaban karamar hukumar Gwarzo da ke Jihar Kano Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya ce zai yi amfani da damar da al\’umar yankin suka ba shi wajen samar da managarcin ci gaba a fadin karamar hukumar ba tare da nuna kasala ba.
Ya yi wannan albishir ne a hirarsu da wakilinmu, tare da jaddada cewa majalisar karamar hukumar Gwarzo tana da kyawawan manufofi na bunkasa wannan yanki musamman ganin yadda Gwamnan Jihar Kano yake bai wa karamar hukumar cikakken goyon baya wajen aiwatar da aikace-aikace na inganta rayuwar al\’uma ta kowane fanni.
Ya ba da misali da yadda aikin samar da ruwa a garin Gwarzo da kewaye yake samun nasarori bisa amincewa da kuma taimakon Gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje kuma a da lokaci kankane, wanda a cewarsa hakan ya sanya yanzu ana samun ruwan sha mai tsafta bayan dadewar da aka yi babu ruwa a famfo duk da cewa Allah ya albarkaci yankin da madatsun ruwa masu tsohon tarihi.
Injiniya Bashir Abdullahi Kutama ya kuma sanar da cewa nan gaba kadan karamar hukumar za ta yi bikin tallafa wa mata da matasan yankin domin su sami sana\’oi na dogaro da kai kamar yadda gwamnatin Jihar Kano ta tsara, sannan za a yi rabon kayan tallafi ga wasu al\’umomi da ambaliyar ruwa ta shafa da ke yankin wanda kudn su ya haura Naira Miliyan arba\’in domin a rage masu radadin asarar da suka yi sanadiyyar wannan ambaliyar ruwa da ya faru.
Bugu da kari, shugaban karamar hukumar ta Gwarzo ya bayyana cewa za a kara inganta rayuwar ma\’aikatan karamar hukumar da samar da kayan aiki da kuma kyautata yanayin guraren aikinsu domin ganin ayyuka suna tafiya cikin nasara da ingantuwar aiki, inda kuma ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa kansilolin yankin da shugabannin sassa na ma\’aikatun karamar hukumar da daukacin ma\’aikatan karamar hukumar saboda haduwa da aka yi ana aikin alheri.
Daga karshe, Injiniya Bashir ya gode wa Gwamna Ganduje da sauran masu ruwa da tsaki na karamar hukumar Gwarzo da shugabannin jam\’iyyar APC na karamar hukumar da na mazabu da kuma uban kasa kuma Hakimin Gwarzo bisa kokarin da ake yi na bunkasa yankin cikin nasara tun lokacin da suka karbi jagorancin majalisar karamar hukumar.