LALACEWAR TARBIYYA AN BUKACI IYAYE SU DAINA LAANTAR YAYAN SU
MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
A wannan mako ne kwamitin wa’azin matasa na kungiyar Izala mai
hedkwata Jos,reshen Jihar Kuros Riba kararkashin shugabancin malam
AUWAL ABDULKARIM , shugaban shiyyar kudu maso kudu ya gabatar da
taro kan sanin makamar aiki ga matasan kungiyar shiyyar jihohin kudu
maso kudu a kalaba fadar gwamnatin kuros riba wakilin mu MUSA MUHAMMAD
KUTAMA ya tattauna da shugaban kwamitin wa’azin matasa na kasa Ustas
Murtala Idris Malwa kan tarbiyya lalacewar tarbiyya laifin na waye.Dama kuma maqalar da shugaban ya gabatar ke nan a kan tarbiyya
.
Ga yadda tattaunawar su ta kasance kamar haka.
GTK:Akramakallahu a makalar da ka gabatar ka yi ta ne a kan tarbiyya,shin
lalacewar tarbiyya wa za a dora wa alhaki?
Ustas Murtala Idris Malwa:To Alhamdulillahi wasallallahu alan Nabiyil
karim,amma ba’ad Assalama alaikum sunana murtala Idris Malwa wanda
ni ne Allah ya kaddara nake jagorantar matasa na kasa abin da ya shafi
kwamitin wa’azin matasa na kungiyar Izala ta kasa mai hedkwata
Jos, wadda Assheik Isma’ila Idris Bn zakariyya ya Assasa Allah ya
jikansa kuma take karkashin jagorancin Assheik Sani Yahaya Jingir
Allah ya kara masa yadda.Da sauran mataimakansa To wannan tambaya da
ka yi gaskiya kowa yana da gudunmawar da zai bayar wajen tarbiya tayi
kyau baza’ace wane ne shi kadai ba kowa zai iya bayar da gudunmawa
Iyaye,sune wadanda suke kashin bayan bayar da tarbiyya,su ne wadanda
wannan nauyi ya rataya wuyansu domin ‘ya’yayen su ne suka haife
su tun suna qanana saboda haka duk abin da za a yi na tarbiyya yana
hannunsu su ne gimshiki na bayar da tarbiyya saboda haka suna da
gagarumar gudunmmawa wajen bayar da tarbiya sune suk da lion share a
ciki [kaso mafi girma] na biyu kuma Hukuma tana da karfi sosai domin
it ace zata yi amfani da karfin mulki ita ce za ta iya sanya wa a yi
kaza-ko abar kaza haka kuma malaman makaranta suma suna da qarfi idan
iyaye suka yi tarbiyya a gida malamai ma suna da karfin gudunmawar da
za su bayar da Allah ya kaddara za su bayar hukuma ita ma to da ikon
Allah za a yi nasara idan akwa haka tarbiyya zata zama ita kamar daukar
daki ne ,sai iyaye sun kama sai malamai suma sun kama sai hukuma ta
kama sai al’umma gabaki daya kowa kama ya yadda za a yi tarbiyya sanna
al’umma ta yi tarbiyya sai Ubangiji ya yi jagora.
GTK: Mene ne malam yake ji ya kawo lalalacewar tarbiyya da ake ta faman kuka a kai?
Ustas murtala Idris malwa:Gurvacewar tarbiyya shi ne abin da ya kawo
shine kowa ya dauki soyayya ya mafi yawanci sun dorawa ‘ya’yayen su
kowa baya son a ce dansa ya yi laifi kowa ba ya son a ce an yi wa dansa fada
kowa bayason ya yi fada a kan tarbiyya na dansa dalili kuwa wani dan
shine yake rike da gidan nasu shi yake fita ya nemo abin da za a ci a
gidan ko ya tallafawa mahaifan da suke kokarin yi musu fada alhali
Allah ya bayar da dama ga wanda ya haifi yara ya tarbiyartar da su
idan mutum ya yi iyakar bakin kokarinsa akai Allah zai taimake shi
komai ya zama ko miloniya ya zama kai uba ne kai ne kake da dammar da
zaka tsawatar masa ka yi kaza kabar kaz ahaka bashi da kyau idan muka
dauki wannna cewa Allah ya dora musu wannan aikin ba ruwansa da tunanin
dan ya samu kudi ko bai samu ba ko rans azai baci ko ba zai baci ba kuma
za a samu nasara haka iyaye mata sai sun tsaya sun jajirce sun bai wa
mazan hadin kai da goyon baya to tari rashin bayar da goyon baya ga
mazajen shi ke kawo lalacewar tarbiyya musamman ta ‘yan mata .
GTK: A zamanance kafafen sada zumuntar nan kana ganin su ma sun taimaka
matuka gaya wajen lalata tarbiyyar al’umma ?
Ustas murtala Idris Malwa: Ai cikin abubuwan da suke faruwa tsakani da
Allah na gurbacewar tarbiyya to su sun dauki kaso mai karfi sun dauki
sama da kashi 50 ko 60 cikin 100.na gurbacewar tarbiyya wani duk yadda
ya kai da tsare gida da tarbiyyar ‘ya’yayen in dai ya yarda ya ba yarinya
waya a hannu ko ya bari wani ya saya mata to yana tufka ne ana
warwarewa idan kana so tarbiyya ta yi kyau to kada ka bari ‘yarka ta
mallaki waya idan zata iya bude babbar waya a hannunta za ta iya budewa
taga fim din batsa wani zai iya kiranta a waya ya ce su hadu a waje
kaza ,wani zai iya yi mata maganganu wadanda tun tana jin kunya wata
rana za ta gano wayewa ce saboda haka wadannan \’social media\’ din
abubuwan da suke yi na alheri yana da yawa amma na sharri ya fi yawa .
GTK: Kai ne shugaban kwamitin wa’azin matasa na kasa mai kungiyar Izala
take yi musamman kwamaitin ka wajen na kowace jiha ya zabura wajen rika
shirya taron sanin makamar aiki kamar yadda reshen kungiyar na Kuros
Riba ya shirya domin a jawo hankalin jama’a da na matasa su kaurace wa
duk wasu abubuwa da ke jawo lalacewar tarbiyya ?
Ustas murtala Idris malwa:To hanyoyin da Alhamdulillahi muke bi ta yin
ayyuka ainihin kamar wanda ya kawo mu nan Kalaba na shirya taron sanin
makamar aiki muna da matasan da sune jagororin jaharsu sai su dora
a duk inda muka tsaya duk jahar da muka je idan mun yi wadan nan ayukan
mukuma muna gaya musu kukuma ga aikinku ga kuma aikin day a kamaku
domin ba mu kullum za mu zo nan ba wata jahar zamu je kuma duk jihar da
mukaje ita zata dauki nauyin abinda za’ayi da ikon Allah duk jihar
da ta dauka sai ka ga tarbiyyar tana ci gaba a kullum muna bai wa juna
shawarwari idan suna da matsala ko wani abu ya shigar musu duhu bayan
mun tafi shugabannin jihar suna kira kuma muna ba su shawara mu warware
musu kuma
GTK: Wane kira za ka yi wa ‘yan siyasa su daina dilmiyar da matasa, suna
ba su kayan maye suna yin yakin neman zabe da su da zarar sun ci moriyar
ganga sai kuma ka ga sun yada kwaure, karshe su buge sara suka shan kayan
maye da sauran nauikan ta’addanci ba ka ganin babban kalubale ne gare
ku tun ma kafin yakin neman zaben 2018 ya kankama a wa’azance ku riqa
fadakar da jama’a dama su ‘yan siyasar ?
Ustas murtala Idris malwa: To Alhamdulillahi wannan ya zama mana rowan
dare dama ba ma ma hutawa koyaushe akinmu kenan yi musu nasiha da
wa’azi da wannan fadakarwa kamar yada ka fada bamu da wani lokaci da
za a ce banda wannan lokacin kullum kawai aikin mu ke nan mu nuna musu
mahimmancin mutum ya tsya yayi karatu kaga wanda ya tsaya yayi karatu
ya dogara ga Allah ya dogara ka kansa yasan ya dogara da aikin da yake
gudanarwa ko sana’a da yake yi ba za ka same shi cikin wadanda ake amfani
da su a kan bangar siyasa ba zaka samesu cikin wadanda za’ace gashi ya
zama dan sara suka ba ko dan kungiyar asiri ba ,ba za ka same shi cikin
wadanda suke tayar da hayaniya ba idan antayar da hayaniya bazaka
same shi cikin harkar da yake yi ba tun da yana da harka wadanda suke
zauna gari banza su ake amfani dasu kuma har yanzu a daida wannan
lokaci ina kira ga su ‘yan siyasa su daina irin wadannan abubuwan dan
ka yana makaranta kai ka dauki dan wani abin da ba ka so a yi maka kada
ka yi ma wani to ka dauki dan wani ka bashi kudi suje su sayi kayan
maye su shay a kawar musu da hankali kaga ai haka masifa ce kuma mian
kayi kaima fa za’a yi maka saboda haka nake kira da suma suji tsoron
Allah su daina bayar da abubuwan don ya zamanto an yi maye an kashe
mutane mutum ma bai san ma ya yi kisan ba sai daga baya a nuna masa
ya yi kisan kai domin ba ya cikin hankalinsa ina kira har yanzu ga
gwamnatoci da ‘yan siyasa kada su zamanto sun yi amfani da matasa wajen
harkar abin da ya shafi matasa wajen kungiyar asiri samun wadanda yake
suna cikin wadan nan kungiyoyi sai suna da ubangida da ke sanya su don
Allah mu tsaya mu yi tarbiyar ‘ya’yayenmu kada a yarda a ba su abin da zai
zamanto musu bala’i .Ba a gane wadan nan matsalolin sai mu da muke
zuwa wa’azi gidajen yari za ka ga rasa abubuwa marasa dadi marasa kyawun
gani .
Wani kana tambayarsa ka san cewa laifinsa ne ya kawo shi gidan
sabodame?saboda wani lokacin ma da ya gudanar d aabin ma baya cikin
hayyacinsa am ba shi tabar wiwi an ba shi giya ,an ba shi sholusho,
lokacinda zai sokawa wani dan uwansa wuka baya cikin hayyacinsa .
GTK:Da ma tambaya ta gaba a kan gidan yari zan yi maka a makalarka ka ce ka
dauko wa wani dan gidan yari alqawari masu karatun jaridar nan za su
zaqu wajen karanta wancan alqawari da ka dauka wace nasiha Malam
zaiyi wa iyaye su rika hakuri da ‘ya’yansu suna tarbiyartar da su ?
Ustas Murtala Idris Malwa: Abinda ya faru na wancan alqawari wani na
gidan yari a wata jihad a bazan ambata sunan taba dana mutumin wato a
wani wuri ne da ake harkar shaye-shaye sai uban wannan mutum ya hana
dansa zuwa wurin sai yaqi jin maganar uban yaje wurin majalisar ta
shaye-shayen ashe ‘yan sanda na nan sun maqe suna jira duk wanda yazo
wurin shi zasu kama ashe anyi kisan kai wurin an rasa kowaye yayi
kisan tsautsayi ya fada kan wannan da bai ji ba-bai gani ba aka kama shi
wasa-wasa sai gidan yari aka yanke masa hukuncin dauri ya samu shekaru
masu yawa yana ciki shi ne ya ce in daukar masa alqari idan duk na zo yin
fadakarwa in isar da sakonsa ga matasa don Allah su rika jin maganar
iyayen su saboda abinda ya faru gareshi rashin jin maganar mahaifns
a ce ta jaza masa to wannan shi ne alqarin fada da isar da sakon na
dauko masa kuma na isar.
GTK: Wace nasiha malam ke dauke da ita ga wasu iyaye da ke la’antar ‘ya;yan su ?
Ustas Murtala Iris Malwa:Gaskiya kiran da zan yi irin abubuwan da muka
samu a gidajen yari da mukaje muka zazzagaya akwai abubuwa marasa dadi
saboda haka zanyi amfani da wannan dama lallai miyaye suji tsoron
Allah idan sukaji tsoron Allah ‘ya’yayen su ba za su shiga wani hali na
lalacewar tarbiyya ba,idan suka ji tsoron Allah bazasu yi musu baki ba
domin idan kayiwa danka baki ka gurbata masa tarbiyya hausawa ma sunce
nagari na kowa amma mugufa ? sai mai shi shi ma Bahaushen a addini ya
samu ko yaushe abinda ake nema ga iyaye idan ‘ya’ya yensu suka saba
musu su ce Allah ya shirye ka/ki wata rana aka cewa Annabi ga abin da
al’ummarka sukayi maka mutane g abinda sukayi maka mai kake so ayi
yanzu kawai ya ce yana roka musu Allah ya shirye su domin idan ba su
shiryu ba ba su sani ba ka ga ai sai ya yi wa alummarsa wannan addu’a.
Wata rana ina karanta wata jarida ta tarihin malamai ta kasar saudiyya
sai nakaranta tarihin mahaifiyar shahararren malamin nan makarancin
Alqur’ani Assheik Assudais cewa wata rana mahaifiyarsa ta tava tafiya
unguwa ta bar shi a gida lokacin yakai mizanin an yaye shi bayan ta dawo
a labariin aka ce ta tarar ya yi mata kaca-kaca da daki to ni zan iya ce
bada misali kamar yanzu a ce ya zubawa buhun shinkafa kananzir maimakon
ta doke shi ko ta la’anceshi kurum baiwar Allah nan sai ta dafa kansa
ta ce Allah ya shiryeka ya sa ka zama limamin makka.Kaga sai Allah ce
mune fiyayyar al’umma saboda haka duk yadda ‘ya’yanka suka kai da
matsala ka yi masu addu’a su ce Alah ya shiryeka/ki akan abinda akayi
idan uwace addu’ar Allah na gode maka da ka ba ni wannan cikin Allah ya sa
in haifi da’’ya wadda take yake mutumin kirki wasu matsalolin wasu
iyayen ke tsinewa ‘ya’yayen tun suna ciki wata uwar ma sai kaji tana
fadi ita tunda take ma bata tava yin tsinannen ciki kamar wannan ba
tun yaron yana ciki ko tace bantava yin shegen ciki ba kamar wannan
cikin wanda yake wahaldani irin wannan cikinan ba ba a haifi ma ‘yar
ko dan bama an masa mugun baki saboda haka idan ta tashi sai a samu
matsala.
Ina kira ga iyaye maza da mata su guji la’antar ‘ya’yansu su ji tsron Allah