Sojojin Nijeriya Sun Yi Wa TY Danjuma Raddi

0
772
Ina Sojojin Suke Ne? Boko Haram A Yobe

Rabo Haladu Daga Kaduna

RUNDUNAR sojin nijeriya  ta yi alla-wadai da kalaman tsohon hafsan sojin  Laftanar Janar Theoplus Danjuma inda ya ce sojojin kasar nan ne ke mara wa Fulani makiyaya baya wajen kawar da al\’ummu a jihar Taraba.
Shi dai Janar Theoplus Danjuma mai ritaya ya yi kalaman ne yayin bikin yaye daliban jami\’ar jihar Taraba da ke Jalingo ranar Asabar.
Ya shawarci al\’ummar Najeriya da su tashi tsaye su kare kansu daga hara-haren makiyaya.
Janar Theoplus Danjuma mai ritaya ya ce \”zaman lafiya a jihar Taraba na cikin wani hali kuma akwai kokarin shafe wata al\’umma a jihar a don haka wajibi mu ta shi tsaye.\”
Tsohon hafsan sojin ya ce idan jama\’a suka zura ido suna jiran sojoji su kare su to za a kashe su daya bayan daya.
Tuni dai rundunar sojin Najeriyar a wata sanarwa, ta mayar da martani ta bakin mai magana da yawunta, Birgediya Janar Texas Chikwu.
Rundunar ta yi alla-wadai da kalaman tsohon hafsan inda ta jaddada cewa rundunar sojin
kasar ce keda alhakin kare rayuka da dukiyoyin \’yan kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here