Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
GAMAYYAR kungiyar Kiristocin tarayyar Nijeriya ta bayyana cikakkiyar gamsuwar da aka samu a bangaren tsaro.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a garin Kaduna a lokacin wani taron manema labarai da ta gudanar a cibiyar Yan jarida reshen Jihar.
Furofesa Adamu Baiki ne ya bayyana gamsuwar lokacin da yake jawabi ga manema labarai, inda ya ce a gaskiya an samu ci gaba a harkar tsaro ba kamar irin yadda lamarin yake a can baya ba.
\”Hakika an samu ci gaba a lamarin tsaro ba kamar yadda lamarin yake a can baya ba, sai dai ya bayar da shawarar cewa yana da kyau a kara inganta lamarin\”.
A game da lamarin sake fasalin tsarin mulkin kasar kuwa da wasu ke kokarin bayyana yadda ya dace a aiwatar kuwa, Adamu Baiki ya bayyana cewa shi baya son cewa a dauki na wannan ko wancan amma dai a aiwatar da duk abin da za a yi ta fuskar yadda Yan kasa musamman ma Talakawa za su samu moriya ta yadda kasa za ta kara inganta.
Sai dai ya fayyace wata matsalar da ke cima jama\’arsu na kiristoci tuwo a kwarya na \”rashin daukar su aiki a wasu jihohin inda za a ce Babu kiristoci a wannan jihar, bayan Kuma kamar yadda kowa ya Sani jama\’a ta karu,gidaje sun Karu Kuma wadannan Kiristocin a Jihar suke zaune a wasu lokutan ma za a iya ganin har kabarin kakanninsu duk suna a wannan wuri amma idan an zo daukar aiki ko bayar da musamman Gwamnati sai ace Babu kiristoci a Jihar\”. Inji Adamu Baiki.