An Cire Kwamishinan Yan Sanda Na Kogi

0
795
I G Na \'Yan Sandan Najeriya
Mustapha Imrana, Daga Kaduna 
SAKAMAKON tserewar da wadansu da ake zargin sun aikata laifi amma suka tsere daga jami\’an \’yan sanda ya sa shugaban \’yan sandan Nijeriya Ibrahim Idris ya cire Kwamishinan \’yan sanda na Jihar Kogi.
Shugaban \’yan sandan Ibrahim Idris ya bayar da umarnin a yi gaggawar cire Kwamishinan \’yan sandan, Ali Janga.
Wannan umarnin dai an bayar da shi ne a yau ranar Laraba 28 ga watan Maris, biyo bayan yadda wadansu da ake zargi da aikata laifi suka tsere daga wajen \’yan sanda a safiyar yau.
Wannan laifi dai ya shafi wadansu manyan \’yan sanda bisa sakacin da suka yi da aiki wanda ba karamin laifi ba ne a samu ma\’aikaci na sakaci da cikinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here