MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga Kalaba
DARURUWAN Mata ne suka fito kan titi birjik a kauyen
Okuni,shekaranjiya Laraba da ke karamar hukumar Ikom jihar Kuros Riba
suka yi zanga-zanga domin nuna fushin su game da zargin jami’an ‘yan
sanda, 5, da suke aikin yaki da ‘yan fashi da makami da aka fi sani
da SARS suke zargin su da yi wa daya daga cikin su fyade a wannan
kauye matan babu inda basu karade ban a titunan garin suna zanga
-zangar lamarin anyi zargi aikata laifin ne tun 6 ga watan Nuwamban
2017, a gonar koko haka nan kuma sun zargi ‘yan sandan das ace buhunan
kokon ,wake duk haka bai ishe su ba sai da suka kama matar mai gonar
suka ji dadi da ita kana suka tafi.
Daya daga cikin matan da suka kwararar kan titin garin Mai suna
Blessing Agan ,ta shaidawa wakilin mu lokacin da akayi cin zarafin
matar da akayiw afyaden asibitin na kauyen kana daga bisani aka
sanarwa da ‘yan sanda a Ikom abina ya faru tace “Abin bakin ciki ma
dubi yadda aka sanarwa da ‘yan sanda amma wanda ake zargin bayan
kamashi sai suka bayar da belins aka kai Magana kotu abin takaici a
watan nan da muke ciki na Maris da aka zauna kotu domin ci gaba da
sauraron karar da alkali ya nemi a gabatar da shaidun asibiti da kuma
na ‘yan sanda sai aka ce fayil ya yi batan dabo ba’a gani bato wannan
dalili ne ya sanya muka fito zanga zanga domin nuna takaicin
mu”inji ta.
Wannan lamari da ya kazanta ya jawo tayar da jijiyoyin wuya tsakanin
al’ummar Okuni , matasan su da kuma sauran masu son a yi adalci a
korafin da suka rubuta takardun koke suka kai babban ofishin yanki na
‘yan sandan Ikom da kuma sakatariyar karamar hukuma suna bukatar
lallai sai a zakulo wanda ake zargi da aikata laifin a hukuntashi .
Mai magana da yawun matan kauyen Olulumoh, kauyen da abinda ake zargi
ya faru mai suna Grace Abini ta shaidawa wakilin mu na kudanci cewa
“gaskiya cin mutuncin da aka yi mana musamman mu mutanen kauyen
Olulumoh ,da akayiwa daya daga cikin mu cin zarafi fyade in fito maka
a mutum muna bukatar sai lallai ‘yan sanda su fito mana da wanda ake
zargi da yin fyaden kana kuma su fito mana da rahoton bayanin likita
day a duba wadda aka yiwa fyaden kana mu samu natsuwa” ita ta fadi
haka.
Wakilinmu ya tuntubi ASP Irene Ugbo, kakakin rundunar ‘yan sandan
jihar kuros riba game da lamarin tace “kada asa garaje komai na nan
ana binsa daki-da daki kuma duk wanda ya saba doka idan aka sameshi da
laifi rundunar bazata taba barin wani shafaffe da mai ba tunda dama
bata dashi.inji Ugbo.