MATASA SUN FAR WA TAWAGAR DAN MAJALISAR WAKILAI TA TARAYYA MAI  WAKILTAR MAZABAR LERE 

0
1123
Shugaban majalisar Dattawan Najeriya, Bukola Saraki

Isah Ahmed, Jos

WASU fusatattun matasa sun farwa dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar  mazabar karamar hukumar  Lere da ke jihar  Kaduna Alhaji Muhammad Lawal  Rabi’u da dan majalisar dokoki ta jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Lere ta yamma Alhaji Bashir Idris Gatari, da dan majalisar dokoki ta jihar Kaduna mai wakiltar mazabar Saminaka Alhaji Abdullahi Idris Marafa da tsohon shugaban karamar hukumar Lere Alhaji Sani Tanimu Saminaka. A kofar wurin da aka gudanar da zaben fidda gwani na kujerar shugaban karamar hukumar Lere na jam’iyyar APC  a karshen makon da ya gabata a garin Saminaka.

Su dai matasan sun farwa wadannan ‘yan majalisa ne, a lokacin da suka zo don shiga wurin da za a gudanar da wannan zabe. Wani da abin ya faru  kan idonsa ya shewada wakilinmu cewa matasan suna ganin tawagar motocin wadannan ‘yan majalisu, sun iso wannan wuri. Nan take suka far masu suka farfasa motocinsu, kafin jami’an tsaro su samu su shiga da su wajen da ake gudanar da zaben.

A yayin da matasa s suka tare tsohon shugaban karamar hukumar ta Lere Alhaji Sani Tanimu Saminaka da bai sami shiga wajen taron ba. Suka far masa da duka har sai da suka kai shi kasa, suka ji masa raunika kafin wasu da suka samu suka kubutar da shi aka kashi asibiti.

Wakilinmu ya ganewa idonsa yadda jami’an tsaro na ‘yan sanda  suka sanya wadannan ‘yan majalisa tare da tawagarsu a motoci suka yi masu rakiya suka fitar da su daga wajen wannan taro.

Wata majiya ta sheda wa wakilinmu cewa matasan sun yi wannan abu ne domin nuna fishinsu kan kokarin da wadannan ‘yan majalisa suka yi, na ganin an canza wajen da aka gudanar da wannan zabe da kuma ‘yadda ‘yan majalisar suka kasa yin ayyukan komai a wannan mazaba.

A wata sabuwa kuma Alhaji Abubakar Buba ya lashen zaben fidda gwani na takarar kujerar shugabancin   karamar hukumar Lere na jam’iyyar APC da aka gudanar a karshen wannan mako da ya gabata.

Da yake bayyana sakamakon zaben, babban jami’in da ya gudanar da zaben Dokta Muhammad Mansur Kayarda ya bayyana cewa a wannan zabe da aka gudanar.

Alhaji Abubakar Buba ya sami kuru’u 233, Alhaji Haruna Bawa ya sami kuru’u 43 a yayinda Debora Iliya ta sami kuru’u 20. Don haka ya bayyana cewa Alhaji Abubakar Buba ne ya lashe wannan zabe, na fidda gwamni na jam’iyyar APC da aka gudanar.

Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan kammala zaben Alhaji Abubakar Buba ya bayyana matukar farin cikinsa kan wannan zabe da aka yi masa.

Ya bada tabbacin cewa idan Allah yasa ya kai shi, ga nasara a zaben da za a gudanar zai cigaba da gudanar da abubuwan alheri da aka faro a wannan karamar hukuma. Kuma zai kirkiro wasu sababbin ayyuka da zasu amfani al’ummar wannan karamar hukumar .

Daga nan ya yi  kira ga wadanda suka yi takara su zo mu hada hanu don su ceci wannan karamar hukuma su raya ta.

Shi ma da yake zantawa da ‘yan jarida shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Lere MalamYunusa  Manu ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka gudanar da wannan zabe lafiya. Ya ce wannan ya nuna cewa jam’iyyarsu ta APC ce zata lashe wannan zaben karamar hukumar Lere,  da za a gudanar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here