YANZU DALIBAI SUN RUNGUMI KARATUN FANNIN NOMA A NIJERIYA-DOKTA NAMAKKA

    0
    902

      Isah Ahmed, Jos

    DOKTA Abdullahi Namakka shi ne  Shugaban kwalegin koyar da aikin gona da ke Samaru ta jami’ar Ahmadu Bello Zariya. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana cewa yanzu dalibai da dama suna gasar shiga kwalegin don karanta fannin aikin noma. Sabanin baya da dalibai suke kyamar karanta fannin aikin noma.

    Har’ila yau ya yi bayanin cewa yanzu noma ya fara bunkasa a Nijeriya domin yanzu kusan kowa ya koma noma. Kuma yanzu kudi ya koma hanun manoma a Nijeriya.Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

    GTK; A wannan lokaci ne aka kafa wannan kwaleji kuma mene ne manufofin kafa ta?

    Dokta Abdullahi Namakka; Wannan kwaleji marigayi Sardaunan Sakkwato Sir Ahmadu Bello ne ya kafa ta, a shekara ta 1961. Sannan kuma wannan kwaleJi ita ce asalin  jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Domin ita ce Sardauna ya fara kafa ginshiKinta, a matsayin kwaleJin aikin gona daga baya ta rikide ta koma jami’ar Ahmadu Bello, da ke Zariya.

    Kuma wannan kwaleji ire irensu guda uku ne  marigayi Sardauna ya kafa, a karkashin jami’ar Ahmadu Bello  a wancan lokacin. Wadannan kwalejoji  guda uku kuwa, sune  bayan wannan kwalejin aikin gona ta Samaru, akwai kwalejin koyar da aikin gona da kiwon dabbobi da ke Mando Kaduna da kuma kwalejin koyar da aikin gona da ke Kabba, a jihar Kogi.

    Manufar kafa wannan  kwaleji ta  koyar da aikin gona ta Samaru, shi ne ta horar da malaman gona wato daliban da wannan kwaleji zata yaye, su zama zakakuran malaman gona da  zasu fantsama cikin dazuka da kauyuka don su koyawa manomanmu dabarun noma irin na zamani. Wannan shi ne ainihin dalilin  kafa wannan kwaleji. Domin  lokacin da Sardauna da sauran masana suka kafa wannan kwaleji sun  sun ga cewa noma shi ne ginshikin tattalin arzikin kasar nan, don haka suka kafa wannan kwaleji da sauran wadancan kwalejoji. Don a rika horar da malaman gona da za su rika shiga lungu lungu da kauyukan kasar nan, don horar da manoma kan dabarun noma irin na zamani, ta yadda za a bunkasa harkokin noma a kasar nan.

    Kuma ita wannan kwaleji ta koyar da aikin gona da ke Samaru Zariya, zalla abin da take koyarwa shi ne aikin gona. Kuma aikin gonar nan ya karkasu  kashi kashi. Misali akwai koyar da dabarun noma na dangin hatsi kamar dawa da gyero da masara da dai sauransu. Haka kuma akwai sashin koyar da dabarun noman itatuwa kamar su lemo da kashu da gwiba da dai saransu. Sannan kuma akwai fannin kiwon dabbobi kamar su shanu da kaji da sauran tsuntsaye da zomaye da kifi.

    Sannan kuma akwai sashin da yake koyar da yadda za a magance cututtukan kwari na amfanin gona. Akwai kuma sashin koyar da aikin girke girke. Wadannan sune abin da wannan kwaleji take horar da dalibai a kai kan matakin ilmi na karamar  Diploma da babbar Diploma.

    GTK; Wace irin gudunmawa ce kake ganin wannan kwaleji take bayarwa wajen bunkasa harkokin noma a kasar nan?

    Dokta Namakka; Gudunmawar da wannan kwaleji take bayarwa  wajen bunkasa harkokin noma tana da yawa. Misali kamar yadda na fada wannan kwaleji tana horar da malaman gona da suke fitowa suke horar da manoma dabarun noma irin na zamani.

    Kuma akwai kamfanoni masu zaman kansu da suke daukar jami’an da muke horarwa a wannan kwaleji don yi masu aiki. Misali kamar kamfanonin  irin shuka da kamfanonin magungunan  kwari da feshi.

    Bayan haka wadanda muke horarwa suna samun kansu a makarantu a inda suke aikin koyarwa kan aikin noma.  Wadannan suna daga cikin irin gudunmawar da muke bayarwa wajen bunkasa harkokin noma a kasar nan.

    GTK; a baya dalibai da dama basa son karanta fannin aikin noma, ganin yadda ake ta kokarin komawa harkokin noma a kasar nan, ya ya abin yake a  yanzu?

    Dokta Namakka;  Wato ada wannan al’amari na yadda dalibai da dama basa son karanta fannin gona ya zama kamar ruwan dare gama duniya. Domin ada idan aka yi maganar aikin noma wato aka ce dalibi yaje ya koyi aikin noma, gani yake yi kamar wata tsohuwar sana’a ce ko kuma yagaggiyar riga da zai dauka ya yafawa kansa ne. Kuma duk inda ya wuce yana ganin abin kunya ne ace gashi yazo yana karanta fannin aikin gona a jami’a. Wato suna ganin noma kamar wata kasashiyar sana’a ce da sai dai mutanen kauye ne kadai za su iya yi.

    Wannan ne ya sa ada kwalejojin koyar da aikin gona basa samun daliban da yawa saboda kallon  daliban suke yiwa wannan fanni na aikin gona.

    Amma yanzu ganin hankali ya koma kan aikin noma kuma an gano wannan fanni yana bayar da guraben ayyukan yi ga matasa. Yanzu matasa sun gane suna ta shigowa wadannan kwalejoji na koyar da aikin noma. A bana sai da muka rage daliban da muka dauka saboda yawansu.

    Kuma wani abin shawa’a shi ne yadda muka dada yin gyare gyare a manhajar da muke koyarwa a wannan makaranta. Yanzu mun juya manhajarmu mun zamanintar da ita ta yadda dalibi idan ya yi karatu, idan ya fito ba sai ya dogara da aikin gwamnati ko aikin kamfani ba. Dalibi zai iya kama sana’ar da zai iya riqe kansa da sauran al’ummar da yake tare da su. Wadannan abubuwa sun taimaka wajen jawo mana dalibai a wannan makaranta. Yanzu za ka ga maza da mata suna zuwa wannan makaranta don karanta fannin aikin gona. Abin mamaki ada kafin kaga mace tana karanta fannin aikin gona da wuya amma yanzu abin mamaki idan kaga yadda dalibai maza da mata  suke gasa, kan shigowa wannan kwaleji don karanta fannin aikin gona abin zai baka mamaki.

    GTK; A matsayinka na masani kan aikin gona ya ya kaga yadda al’ummar Nijeriya suka rungumi aikin gona musamman a wannan lokaci da wannan gwamnati ta ce a koma  gona?

    Dokta  Namakka; A gaskiya yanzu an sami cigaba kan aikin noma a Nijeriya. Domin idan ka kalli harkokin noma yanzu a Nijeriya ka kuma wai ga baya ka kalli harkokin noma a Nijeriya, babu shakka za ka ga cewa yanzu an sami cigaba kan harkokin noma a Nijeriya. Musamman wannan gwamnati da ta fito ta ce a bada fifiko ga aikin noma.

    Magana ta gaskiya hatta wanda baya noma a da yanzu ya rungumi noman nan.  Misali idan ka dauki bara da amfanin gona ya yi daraja kowa za ka ya shiga harkar noman nan. Kuma idan ka dubi harkar noman nan za ka ga shi kadai ne yake jawo duk wani mutum da yake wata sana’a. Misali ka dubi likitoci d a sojoji da ‘yan sanda da injiniyoyi da malaman jami’a duk sun shigo aikin noma.

    Duk wanda ka san yana yin wata sana’a ko yana aiki a gwamnati ko wani kamfani mai zaman kansa ko wata ma’aikata, bana ya shigo aikin noma. Kabga an ci gaba a aikin noma a Nijeriya.

    Yanzu wani abin mamaki kudi ya koma hanun manoma a Nijeriya. Yanzu za ka a Nijeriya manomi ya bugi kirji ya shiga gida ya fito maka da kuxi naira miliyan daya zuwa miliyan biyu zuwa miliyan uku kai tsaye. To ka ga kuwa an cigaba kan aikin noma a Nijeriya.

    Sai dai akwai bukatar gwamnati ta jajirce ta kara zamanantar da noma a Nijeriya. Domin yanzu idan ka dubi tsarin hukumomin bunkasa harkokin noma na kasar nan, za ka ga cewa yanzu babu malaman gona.

    kwanakin baya na tafi jihar Koras Riba na yi ta tambaya kan malaman gona amma ko malamin gona guda xaya ban gani ba.

    Don haka gwamnati ta shigo a dawo da malaman gona  a inganta su yadda za su rika shiga lungu lungu da kauyuka suna horar da manoma dabarun noma irin na zamani. Domin babu yadda za ayi gwamnati ta bunkasa aikin gona ta haryar kafofin watsa labarai kadai. Dole sai malaman gona sun shiga lungu lungu da kauyuka sun wayar da kan manoma sun koyar da su a aikace.

    Sannan kuma gwamnati ta hada hanu da masu hali domin a kafa masana’antu da kamfanoni na sarrafa kayayyakin amfanin gona a kasar nan a rika fitarwa zuwa kasashen waje.

    GTK; Wanne kira ko sako ne kake da shi zuwa ga gwamnati kan tallafa wa irin wadannan kwalejoji na koyar da aikin gona saboda mahimmancin da suke da shi wajen bunkasa harkokin noma a kasar nan?

    Dokta Namakka; Maganar gaskiya tallafa wa kwalejojin koyar da aikin gona yana da matukar mahimmanci. Don haka muna kira ga gwamnati kan ta shigo ta tallafawa wadannan kwalejoji ta hanyar basu goyan baya tare da tanadar masu da abubuwan da suke bukata. Kamar azuzuwa da dakunan bincike da na’urorin bincike na zamani da  motocin noma  da dai sauransu.

    Sannan kuma gwamnati ta taimaka masu da wadatattun kudaden gudanar da harkokin yau da kullum.

    Yanzu misali idan ka duba zaka ga akwai wasu irin na’urori da yake tun zamanin turawa ake aiki da su, har yanzu irin waxannan na’urori ne ake amfani da su a wadannan kwalejoji. Yanzu kuma zamani ya canza kullum ana samun ci gaba. Don haka muna son gwamnati ta shigo ta taimakawa wadannan kwalejoji, su sami kayayyakin aiki irin na zamani da kudade don su samu su mike da kafafunsu su tsaya su yi gogayya da sauran kwalejojin horar da aikin gona na kasahen duniya.Yanzu misali a watan sha daya na wannan shekara da ta gabata naj e Habana babban birnin  kasar Cuba taro kan aikin gona. Wani abin ban sha’awa wannan taro da muka je a wata kwalegin aikin gona ne aka gudanar da shi. Idan ka ga yadda suke koyar da yadda ake hada maniyyin shanu mace da namiji don a sami shanun da suke bayar da madara mai tarin yawa abin zai baka mamaki. Ya kamata muma a rika tallafa mana don mu rika gudanar da irin wadannan abubuwa.

     

     

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here