ZA MU FARFADO DA KUNGIYOYIN ZABI SONKA-BALA MAI KWAKYARA

0
820

Jabiru A Hassan, Daga Kano.

WANI fitaccen dan zabi sonka,  Alhaji Bala Na Sani mai kwakyara ya ce za su sake farfado da kungiyoyinsu na zabi sonka domin karfafa zumunci tsakanin ‘ya’yan kungiyoyin da ke fadin kasar nan dama sauran kasashe makwabta da ke cikin ire-iren wadannan kungiyoyi.

Ya yi wannan albiahir ne cikin wata hira da auka yi da wakilinmu, inda kuma ya sanar da cewa kungiyoyin zabi sonka da taimakon juna sun taka muhimmiyar rawa wajen sada zumunta da hada kan al\’uma da kuma taimaka wa gwamnatoci wajen isar da sakonnin ahirye-shiryensu na ci gaban al\’uma.

Alhaji Bala na Sani mai kwakyara ya kuma nunar da cewa lokaci ya yi da  za a sake farfado da harkar zabi sonka saboda yawaitar kafafen yada labarai na ciki da wajen kasar nan, sannan akwai bukatar a kara samun hadin kan kasa da zumunci kamar yadda manufofin kafa wadannan kungiyoyi.

Haka kuma ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga fitattun ‘yan zabi sonka da suke raye da su hada hannu wajen hada ‘yan zabi sonka domin kulla sabuwar tafiya da zumunta kamar yadda  abin yake a baya, inda kuma ya mika sakon gaisuwar sa ga daukacin ‘yan zabi aonka na kasa wadanda lokaci ba zai bari a bayyana su duka ba.

Daga karshe,  Alhaji Bala na Sani ya yi fatar cewa nan gaba kadan za a fara gudanar da tarurruka na farfado da kungiyoyi na zabi sonka da taimakon juna ta yadda zumunci zai kara dawwama tsakanin ‘ya’yan kungiyoyin mazan su da mata, sannan ya yaba wa mutane irin su Alhaji Auwalu Rimi mai shadda Sabo Shagamu, da shugaba Abdulrazaku na kasuwar Sabon Garin Kano da Ya\’u Bagobiru daci da sauran wadanda ake hulda da su tun lokaci mai tsawo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here