An Kama Yar Shekaru 19 Da Kwayoyi A Cikin Rigar Nono

0
1572

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

JAMI\’AN hukumar yaki da fataucin miyagun Kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen Jihar Katsina sun Kama wata yarinya mai shekaru sha tara, mai suna Zakiya Abdulkarim, dauke da miyagun Kwayoyi a cikin rigar Nono da kuma wasu sassan jikinta.

Kwamandar hukumar reshen Jihar Katsina Uwargida Maryam Sani, da ta tabbatar da Kama Yarinyar mai shekaru sha Tara, ta ce an Kama Yarinyar ne dauke da wadannan Kwayoyi a rukunin gidaje na Sakkwato Rima da nufin ta sayarwa masu hulda da ita.

Sani ta kara da cewa Yarinyar ta gudo ne daga kauyensu domin ta zauna tare da saurayinta bisa dalilin cewa wai za a aurar da ita ga wani ba da saninta ba.

Hukumar NDLEA din dai ta bayar da kididdigar yawan miyagun Kwayoyi da aka samu Yarinyar da su a kan cewa sun kai giram sha hudu da digo hudu na Tiramol, giram sha biyar da digo Takwas na Exol- 5 da kuma giram biyu da digo hudu na maganin sa bacci D5.

Da take ganawa da manema labarai Yarinyar ta shaida masu cewa, saurayinta Abdusalam, ya bata kwayoyin ta AJIYE mashi domin ya mance da wani Abu a gida Kuma yana son ya dauko.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here