Rundunar ‘Yan sandan jihar Kuros Riba ta ce ta karbo makamai 325 daga hannun bata gari dake sassa daban daban na jihar. Da yake gabatar da dimbin makaman ga manema labarai,a harabar ofishinsa cikin su akwai wakilinmu na kudanci Hafiz Muhammad Inuwa kwamishinan ‘yan sandan ya ce sun samu wannan nasara ce a samamen da rundunar ta rika kaiwa ce maboyar su da aka kyankyasa mata.
A wannan hoto da Wakilinmu Musa Muhammad Na Kutama Katsina ya aiko mana da su za a iya ganin nau\’in bindigogin