Rabo Haladu Daga Kaduna
DAGA cikin buhuhunan shinkafa dubu 12 da hukumar kwastan ta kama a kan iyakar Seme ta lalata dubu biyu da suka lalace.
Buhuhunan shinkafa dubu biyun da hukumar kwastan ta lalata na cikin kimanin buhunhuna dubu 12 da ta kama a \’yan watannin nan.
Shugaban hukumar ta kwastan dake kula da iyakar kasa ta Seme Kwanturola Muhammad Aliyu na yankin Badagry ya shaida wa manema labarai. Inji shi ga wanda bai sani ba, shinkafar ta dade ajiye har ta lalace.
A cewarsa idan sun kama shinkafa sukan duba su ga mai kyau da mara kyau domin su ware su daban. Ita mai kyau ita ce ake kai wa sansanin \’yan gudun hijira domin a taimaka masu. Mara kyau sai su gaya wa Abuja domin ba da shawara. Sai a gaya masu su kira hukumar da ke kula da abinci da abin sha wato, NAFDAC. Sakamakon
binciken da ita hukumar NAFDAC ta aiwatar ya nuna ko dabba ma bai kamata ya ci shinkafar ba balantana mutum.
Mista Sunday Ona Oche mataimakin darakta na hukumar NAFDAC su ne suke taimakawa wurin binne gurbatacen abinci,ko abin sha ko magani. Ya kara da cewa tare da hadin gwiwar kwastan da sauran mahunkunta da ke yankin suna tafiyar da ayyukansu kamar yadda ya kamata domin hana shigowa da haramtattun
kaya musamman abinci da kwayoyi ko magunguna.
Sai dai mutanen da ke zaune a yankin sun dauka yin sumoga hakkinsu ne dalili ke nan da suke yakar hukumar kwastan da makamantansu.
Bayan shinkafa hukumar kwastan ta kama motoci dankare da atamfofi. Kodayake shigowa da atamfa ba laifi ba ne amma sai an biya haraji.