Kasar Rasha Ta Yafe Wa Kasashen Afrika Bashi

0
719
Bayanai daga kasar Rasha na cewa shugaba Vladimir Putin ya bayyana cewa kasarsa ta Yafewa Kasashen Afrika bashin Dala biliyan 20
Wannan wata alamace na taimakawa yankin domin ya fita daga matsalar Talaucin da suke ciki shi yasa aka dauki matakin yafe bashin.
\”Tsari ne na taimakawa kasashen Afrika domin su fita daga cikin matsalar Talaucin da suke ciki Kuma mafiyawan kasashen na fama da matsalar bashi,don haka muka yanke hukuncin Yafewa Kasashen kudi Dala biliyan Ashirin Wanda kasashen da dama za su amfana\”. Inji Putun. Kamar yadda kafar labarai ta Rasha ta ruwaito.
Shugaban na Rasha ya bayyana hakan ne bayan taron tattaunawar da suka yi da shugaban kasar Guinea Alpha Conde.
Vladimir Putin ya kara da cewa a shekarar 2016 kasar Rasha ta bayar da Dala Miliyan biyar ga kasashen Afrika ta hanyar kungiyar hadin kan kasashen Afrika abinci da ayyukan Noma ( AUUNFAO).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here