KIMANIN MAKAMAI 324 RUNDUNAR \’YAN SANDAN KUROS RIBA TA KWATO

0
652
I G Na \'Yan Sandan Najeriya
MUSA MUHAMMAD KUTAMA Daga kalaba
RUNDUNAR ‘Yan sandan Jihar Kuros Riba ta ce ta karbo makamai 325  daga
hannun bata gari dake sassa daban daban na Jihar.Da yake gabatar da dimbin
makaman ga manema labarai,a harabar ofishinsa  cikin su akwai wakilinmu na
kudanci Hafiz Muhammad Inuwa kwamishinan ‘yan sandan yace sun samu wannan
nasara ce a samamen da rundunar ta rika kaiwa ce maboyar su da aka
kyankyasa mata.
Kwamishinan har wayau yacerundunar ma tayi sa’ar cafke wasu da ake zargi da
aikata laifuka daban daban  da suka hada da  fyade cikin su akwai ma  wanda
yayi wa wata karamar yarinya ‘yar shekara 9 da haihuwa da kuma hada baki
zamba cikin aminci fashi da makami da sauran aiyuka na ta’adanci.
Hafiz Muhammad Inuwa ya kara da cewa  daga cikin wadanda aka kamaakwai
wanda aka kama  yana zambatar rundunar tsaro ta farin kaya wato sibil
difens da ta ‘yan sanda yana karbar kudade hannun jama’a yana cewa za’a
dauke su aiki.kwamishinan ‘yan sandan ya gargadi al’ummar jihar da duk wani
wanda yasan yana ajiye ko rike da makami ba bisa ka’ida ba ya mutunta kansa
cikin ruwan sanyi ya mika makaminsa kafin doka tayi aiki kansa.
Ya yaba wa kwazon jami’ansa da suke aiki tukuru ba dare ba rana wajen wanzar
da tsaro yace rundunar sa bazata taba yin kasa a gwiwa ba wajen yin maganin
duk wani bata gari .Rundunar ma ta nada kwamitin mutum shida da zasu yi
aikin karbar makaman da ake dasu ba bisa ka\’ida ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here