Masu satar shanu 700 sun tuba

0
651
I G Na \'Yan Sandan Najeriya

Rabo Haladu Daga Kaduna

RUNDUNAR \’yan sanda a jahar Kaduna
ta ce ta sasanta da wasu daruruwan \’yan ta\’adda
da barayin shanu.
A \’yan shekarun nan dai \’yan ta\’addan sun rika
addabar jama\’ar jihar har ma da na wasu jihohi
makwabta.
Rundunar ta kuma ce daruruwan \’yan kwanta-
kwanta, ciki har da masu garkuwa da mutane
sun ajiye makamansu.
An dai yi hakan ne bayan rantsuwa da suka sha
da alkawarin cewa ba zasu koma cutar da jama\’a
ba.
Rundunar dai ta ce za ta ci gaba da bibiyar
wadannan mutane don tabbatar da tuban na su.
Kakakin rundunar ta \’yan sanda ya ce kimanin
mutane 700 ne masu satar shanu da sace-sace
suka tuba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here