SANA\’AR FAWA TANA SAMAR DA AIYUKAN YI  DA BUNKASA TATTALIN ARZIKIN KASA  -SARKIN FAWAR BADUME

    0
    721

    Jabiru A Hassan, Daga Kano.

    SARKIN fawar Badume Alhaji  Muhammadu Danfulani ya ce sana\’ar su ta fawa tana daga cikin sana\’o in da ke samar da guraben ayyukan yi da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa saboda albarkar da ke cikin ta.

    Ya yi wannan tsokaci ne a zantawar su da wakilinmu a mayankar kasuwar Badume, inda ya nunar da cewa akwai dimbin matasa da sauran al\’umar da ke samun abinci ta hanyar fawa tun daga sayen dabbobin yankawa har zuwa gasa nama ko kuma safarar su zuwa wasu sassa na kasar nan.

    Sannan ya bayyana cewa sana\’ar fawa ta kasance a sahun gaba wajen hada kan al\’uma walau a kasuwanni ko a mayanka inda masu wannan sana\’a ke zuwa suna sayen nama zuwa sassa daban-daban, wanda hakan abin alfahari ne da dukkanin masu sana\’ar fawa.

    Alhaji Muhammadu Dan fulani ya yi amfani da wannan dama inda ya yaba wa shugaban karamar hukumar Bichi Alhaji Sani Mukaddas da ‘yan majalisarsa, saboda yadda ake tafiyar da ayyukan alheri a karamar hukumar ta Bichi bisa la\’akari da bukatun al\’umar wannan yanki, tare da yin roko ga karamar hukumar da ta kara sabunta mayankar kasuwar Badume da samar da ruwa domin ta ci gaba da aiki kamar yadda ake bukata.

    A karshe, Alhaji Dan fulani ya yi fatan alheri ga dukkanin masu sana\’ar fawa da ke kasar nan tare da fatan Allah ya kara albarka a wannan sana\’a domin  kyautata tattalin arzikin kasa da na al\’uma kamar yadda lamarin yake a yanzu.

     

     

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here