\’YAN NIJERIYA SUN KOSA DA JAM’IYYUN PDP DA APC -SADEEQ MUSALLA  

  0
  747
  Alhaji Sadeeq Ibrahim Musalla(1)

   Isah Ahmed, Jos 

  ALHAJI Sadeeq Ibrahim Musalla tsohon shugaban riko na kasa na jam’iyyar AFGA ne kuma a yanzu shi ne  sakataren jam’iyyar United Progressive Party,  UPP na kasa. A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya sun kosa da jam’iyyun PDP da APC saboda basu cika alkawuran da suka yi wa ‘yan Nijeriya ba.

  Har ila ya yi bayanin kan yadda yake kallon yanayin siyasar Nijeriya a halin yanzu da kuma shirye-shiryen da jam’iyyarsu ta UPP take yi don tunkarar zabubbuka na shekara ta 2019. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

  GTK; Ganin cewa zabubbukan shekara ta 2019 suna kara gabatowa ya zuwa yanzu wadanne irin shirye-shirye kuka yi don tunkarar wadannan zabubbuka?

  Sadeeq Musalla; Abubuwan da muka sanya a gaba shi ne rajistar ‘yan takararmu da za su yi takarar a wadannan zabubbuka masu zuwa na shekara ta 2019.  Ko  a makon da ya gabata, akwai Mista Daniel Akinlami da ya zo ya nemi mu ba shi dama ya tsaya takarar shugabancin Nijeriya karkashin wannan jam’iyya. Kuma  akwai Farfesa Moghalu wanda shi ma tuni ya zo ya bukaci mu ba shi dama ya yi takarar shugabancin kasar nan.

  A takaice muna da ‘yan takara da damar a kujerar shugaban kasa da gwamnoni da ‘yan majalisun tarayya da ‘yan majalisun jihohi, da muke ta yin rajistarsu.

  A karshe dole ne za mu yi zabubbukan fidda gwani a wannan jam’iyya a takarar kujeru daban-daban.

  GTK; Ganin manyan jam’iyyun  APC da PDP da ake da su a kasar nan, kana ganin wannan sabuwar jam’iyya taku ta UPP, za ta yi tasiri a wadannan zabubbuka na shekara 2019?

  Sadeeq Musalla; Babu shakka wannan jam’iyya ta UPP za ta yi tasiri a zabubbuka na shekara ta 2019. Domin idan ka dubi jam’iyyar PDP jama’ar Nijeriya ba sa yayinta  a  yanzu. Haka ita ma jam’iyyar APC  jama’a sun dauka daga zuwan ta,  za a sami canjin da ake bukata. Amma  a gaskiya ya zuwa yanzu ba a sami wannan canji da ake bukata ba. Wannan ya sa jama’a suna neman sababbin jam’iyyun da za su tafi.

   Don  haka muke kokarin mu kawo mutanen da za su kawo canji na gaskiya da ake bukata a Nijeriya a wannan jam’iyya.

  Domin  jam’iyyun APC da PDP  sun gwada rawarsu amma jama’a ba su gamsu da rawar da suka taka ba.

  Kuma ko a kwanakin baya  idan ka dubi irin rawar ganin da wannan jam’iyya ta UPP ta taka a zaben kujerar gwamna na jihar Anambara a cikin jam’iyyu 37 da suka shiga wannan takara jam’iyyarmu ce ta zo ta 4. Duk da irin magudin da aka yi a wannan zabe.

  GTK; A takaice mene ne manufofin wannan jam’iyya?

  Sadeeq Musalla; Manufar wannan jam’iyya shi ne kawo canji na gaskiya a Nijeriya. Saboda abubuwan da ke faruwa a Nijeriya, ya sanya mutane da dama suna nuna kosawarsu da irin tafiyar da gwamnatin  jam’iyyar APC take yi a Nijeriya. Saboda haka suke neman, a kawo jam’iyyar da za ta kawo canji na gaskiya a Nijeriya.

  Domin yanzu idan ka dubi maganar yaki da cin hanci da rashawa da ake yi a Nijeriya. Har yanzu babu wani canji da aka samu. An kama mutane da dama an ce sun yi sata, amma har yanzu an kasa hukumta su. Yanzu idan kana tafiya a Nijeriya kana kallo za ka ga yadda jami’an tsaro suke karbar kudade a wurin jama’a kan hanyoyin kasar nan. Ga miyagun abubuwa nan suna  ta ci gaba da faruwa.  Duk wadannan abubuwa ne da ya kamata a ce an sami canji a kansu. Don haka dole ne a sami canji na gaskiya a Nijeriya.

  GTK;  Ya ya kake kallon yadda yanayin siyasa yake tafiya a kasar nan, a halin yanzu?

  Sadeeq Musalla; Siyasa tana sake salo a Nijeriya. Domin misali abubuwan da suka fara fitowa na ‘yan majalisun kasar nan. Yanzu jama’a da yawa suna son a soke majalisar dattawa, abar majalisar wakilai ta tarayya kadai.

  Ni kaina na goyi bayan a sako majalisar dattawa domin suna aiki iri daya ne da majalisar wakilai.  Idan aka soke majalisar dattawa kasar nan za ta sami tafiya mai dadi. Idan ka dubi kasashe da dama a duniya, sun dauki irin wannan mataki na soke ‘yan majalisar dattawa. Saboda haka mu ma lokaci ya yi da za a sako majalisar dattawa a Nijeriya.

  GTK; Yaya kake kallon rikice rikicen Fulani makiyaya da manoma da ake fama da shi a Nijeriya?

  Sadeeq Musalla; Wato rikice-rikicen Fulani makiyaya da manoma abu ne da aka fara yinsa tun iyaye da kakanni. Amma ba a taba mayar da shi siyasa ba, sai a wannan lokaci na gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari. Kuma wadanda suka mayar da wannan rikice rikice na siyasa, sun ga babu hanyar da za su iya hana wannan gwamnati sakewa, sai ta wannan hanya. Saboda shi shugaban kasa Buhari bafulatani ne, don haka  bari su yi, ta ruru wutar wadannan rikice-rikice domin su hana wannan gwamnati sakewa.

  GTK; Wanne sako ko kira ne kake da shi zuwa ga ‘yan Nijeriya musamman ganin yadda zabubbukan shekara ta 2019 suke kara gabatowa?

  Sadeeq Musalla; To abin da nake son jama’a su fahimta, shi ne su tantance mutanen da za su zaba a wadannan zabubbuka masu zuwa. Domin hausawa suna cewa auren baya, sadakin na gaba. Don haka mu duba mutanen da muka zaba a baya, shin sun yi mana ayyukan da suka ce za su yi mana. Idan ba su yi mana ba, mu sake tantance wadanda za mu sake zaba. Domin mu sami mutanen da zasu taimaka wajen gyara kasar nan.

   

   

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here