Daga Usman Nasidi
HUKUMAR hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa a ranan Asabar, 7 ga watan Afrilu ta damke wani dan damfara mai suna, Samson Otuedon, a unguwar Masaka, dake karamar hukumar Karun a jihar Nasarawa.
Samson ya kware wajen hada kudaden bogi wand ya kasance yana damfaran jama’a. hukumar ta samu labari akan shi ne rana Juma’a, 6 ga watan Afrilu kawai sai ta far masa ba tare da bata lokaci ba.
An damke shi da sabbin kudade akalla $400,000 (Dala dubu dari hudu). Yayinda ake gudanar da bincike akansa, ya bayyana cewa wasu abokan aikinshi da ke Legas ne suka bashi kudin.
Hukumar ta bayyana cewa za ta gurfanar da shi muddin an kamala bincike.