JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
KUNGIYAR ci gaban karamar hukumar Dambatta wadda aka fi sani da \” Dambatta Development Network\” ko kuma DDN, zata ci gaba da gudanar da aiyukan taimakon al\’uma a kowane lungu da sako na fadin karamar hukumar kamar yadda manufofin kafa ta suke.
Wannan albishir ya fito ne daga shugaban kungiyar Kwamared Adamu Sani Dambatta a wata ganawa da suka yi da wakilin mu a kano, inda ya sanar da cewa an kafa kungiyar DDN bisa aniyar taimakawa al\’umar yankin karamar hukumar Dambatta, tareda gudanar da wasu muhimman aiyuka na inganta rayuwar al\’uma bisa la\’akari da bukatun kowane bangare.
Kwamared Adamu Sani Dambatta ya kuma nunar da cewa kungiyar su tana duba bukatun al\’uma ne domin samun damar aiwatar masu da wasu aiyuka wadanda suke da matukar muhimmanci a garesu, inda kuma ya bayyana cewa tun da aka kafa wannan kungiya ta DDN take gudanar da aikace-aikace na alheri domin kyautata zamantakewa da bunkasa hadin kai tsakanin al\’umar kasar Dambatta kamar yadda ake gani a yau.
Haka kuma shugaban kungiyar ta DDN ya sanar da cewa zasu fara hada hannu da manyan kungiyoyi na duniya wajen gudanar da manyan aiyuka a yankin karamar hukumar ta Dambatta, sannan akwai fannoni masu yawa da suka sanya cikin jadawalin abubuwan da zasu yi domin taimakawa gwamnatoci wajen samar da ababen more rayuwa ga al\’uma musamman a wannan lokaci da abubuwa suka yiwa gwamnatocin yawa.
Bugu da kari, Kwamared Adamu Sani yayi amfani da wannan dama inda ya nuna farin cikin sa ga sauran shugabanni da daukacin mambobin kungiyar ta DDN, saboda yadda aka hada kai ana aiki domin ci gaban yankin karamar hukumar Dambatta, tare da jaddada cikakkiyar godiyar kungiyar ga al\’umar karamar hukumar ta Dambatta saboda goyon bayan da suke baiwa kungiyar DDN.
Sannan ya yi kira ga dukkanin \’yan asalin karamar hukumar Dambatta da suke zaune a ciki da wajen kasarnan da su shigo cikin al\’amuran kungiyar wajen ganin ana cimma nasarori wajen aiwatar da muhimman aiyuka ga al\’uma ta kowane fanni.
Daga karshe, Kwamared Adamu Sani Dambatta ya isar da sakon taya murna a madadin kungiyar DDN ga sabbin shugabannin karamar hukumar Dambatta bisa lashe zaben da suka yi a watan Fabrairu, tareda jinjinawa tsohon shugaban kungiyar ta DDN Kwamared Musa Sani Dambatta wanda ya sami ci gaba zuwa mukamin mataimakin shugaban karamar hukumar Dambatta.
Wakilin mu wanda ya tattauna da mutane daban-daban a karamar hukumar ta Dambatta ya ruwaito cewa kungiyar DDN ta gudanar da aikace-aikace masu tarin yawa kuma a fannoni kamar ilimi da samar da ruwan sha ta hanyar gyaran rijiyoyin burtsatse masu yawa da fannin kula da lafiya da taimakon marasa karfi da sauran aiyuka na jin kai kamar yadda aka gani.
Sannan mafiya yawan mutanen da suka zanta da wakilin namu sun yi kira ga manyan kungiyoyi na duniya masu rajin taimakon al\’uma dasu hada hannu da kungiyar DDN ta yadda zata kara samun damar aiyatar da muhimman aiyuka ga al\’uma a kowane lungu da sako na karamar hukumar ta Dambatta.