\’YAN DABA SUN TABKA BARNA A OFISHIN YAKIN NEMAN ZABEN ATIKU

  0
  562
  Daga Usman Nasidi

  WASU matasa da ake zargin \’yan sara-suka ne sun kai farmaki ofishin yakin neman zaben Atiku da ke kan titin Dandagoro a garin Katsina tare da lalata motocin dake harabar ofishin.

  \’Yan dabar sun kai farmakin ne a karshen mako kuma sun rufe jama\’ar da ke ofishin da duka.

  Jacob Dickson, kakakin kungiyar yakin neman zaben Atiku shiyyar Arewa maso yamma ya ce, \’yan dabar sun lalata dukiyar miliyoyin Naira yayin farmakin da suka kai.

  Aliyu Abbas, shugaban wata kungiyar magoya bayan Atiku a jihar ya bayyana abinda matasan suka aikata da cewar ta\’addanci ne a kan jama\’ar dake ofishin.

  Wani shaidar gani da ido ya ce, \’yan dabar sun zo ne cikin babura masu kafa uku guda uku sun fara ganin abinda ke faruwa a ofishin kafin daga bisani su kawo farmakin.

  Magoya bayan Atiku a jihar na zargin cewar \’yan dabar sun kawo masu harin ne saboda a ofishin da aka yi taron gangamin jam\’iyyar PDP na shiyyar arewa maso yamma.

  Magoya bayan Atikun sun ce sun sanar da ofishin \’yan sanda na Batagarawa abin da ya faru kuma tuni hukuma ta fara binciken lamarin.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here