Kwastan Sun Tara Biliyan 4.3 A Matsayin Haraji

0
621
Shugaba Muhammadu Buhari ne yake jaddada niyyarsa ta sake tsayawa takara a 2019

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

JAMI\’AN hukumar Kwastan shiyyar Kano da suke kula da Kano da Jigawa sun tara kudi naira biliyan 4.3 a matsayin haraji watannin Janairu da Maris na wannan shekarar.

Kwamandan Mista Abbas Alkasim, ne ya bayyana hakan a ranar jama\’ar da ta gabata domin fayyace ayyukan da suka yi a watanni uku na farkon shekara.

Ya ce wannan kokari har ya wuce irin yadda ya dace su tara saboda an ba su yawan kudin da yakamata su tara na biliyan 3.6 inda suka tara kudi naira biliyan 4.3 a watanni uku na farkon shekara.

Kamar yadda ya bayyana sun kuma samu nasarar kame kaya har sau 41 duk na kayan da aka hana a shigo da su Wanda kayan sun kama na kudi naira Miliyan 170.

Kayan da aka kama sun hada da Shinkafa,man girki,Taliya da Makaroni, sukari ,kayan Gwanjo da tsofaffun Motoci.

Kasim ya ci gaba da cewa a ranar Lahadi daya ga watan Afrilu sun samu nasarar kama kayan da aka hana shigowa da su a Jigawa da Kano.

Kayan sun hada da buhunan shinkafa dari biyar da aka boye a buhunan wake sai kuma dilolin tsofaffin kayayyaki 20 da aka Kama a cikin Kano.

Sauran kayan da aka kama a kan iyakar Kantakara wani kauye ne tsakanin iyakar Maigatari da jamhuriyar Nijar.

Ya kuma ci gaba da bayanin cewa an kama mutane hudu bisa wannan aiki ana kuma ci gaba da bincike domin kamo wadanda suka tsere.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here