Daga Usman Nasidi
MUN samu rahoton cewa wani ibtila\’i ya afka wa wata mahaifiya Uwargida Olubunmi Olaitan, yayin da ta yi kacibus da gawar \’ya\’yayenta biyu cikin Firiji a gidan su mai lamba shidda a unguwar Eyin Ala ta birnin Akure na jihar Ondo.
Mahaifiyar wannan yara, Olufemitan dan shekara 9 da kuma Oluwafifunmi dan shekara 7, ta gamu da mugun gani yayin da ta tsinci gawar \’ya\’yanta maza daskare a cikin Firijin.
Rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari ya afku ne a ranar Litinin din da ta gabata yayin da Uwargida Olubunmi ta fita ta bar yaran nata biyu suna wasanni inda dawowarta ke da wuya ta yi kacibus da mugun gani.
Kakakin \’yan sanda na jihar Mista Femi Joseph, ya tabbatar da afkuwar wannan lamari na kaddara mai ban tausayi.
Mista Femi ya yi bayanin cewa, babu wata alama da take nuna kashe yaran aka yi, sai dai ya yi hasashen cewa ta yiwu kiriniya irin ta yara ta sanya wasa ya kai su ga shiga cikin Firijin kuma suka gaza budewa yayin da murfinsa ya rufe da su.