Taurin Bashi: A Katsina Za A Rufe Ofishin Glo

    0
    711

    Mustapha Imrana Abdullahi

    GWAMNATIN Jihar Katsina ta bayyana cewa sakamakon tsananin taurin bashin da kamfanin wayar salula na GLO yake da shi a halin yanzu an ba kamfanin wa\’adin sati daya ko a rufe ofishin.

    Bashin dai ya kai na Naira Miliyan dari hudu da kamfanin ya kasa biya tun shekaru hudu baya duk da irin yadda hukumar gwamnatin Jihar Katsina mai alhakin ganin an biya kudin ta ba kamfanin lokaci amma ya kasa biya.

    Kasancewar ofishin na GLO shi ne na 105 hakika a halin yanzu yana fuskantar barazana kamar yadda Janar Manajan hukumar kula da tsara burane na Jihar Katsina, Usman Nadada ya ce kudin da kamfanin ya kasa biya na shekaru hudu ne da ta gabata, saboda karshen biyan da kamfanin ya yi  tun a shekarar 2014 ne har yanzu ana ta kai ruwa rana ne.

    Kamar yadda Nadada ya bayyana gwamnatin jihar ta bi duk hanyoyin da ya kamata domin a biya ta kudin ta amma hakan bai yiwuwa ba.

    Ya ce an dai ajiye ka\’ida ne kowane watan daya na Bature a biya kudin amma hakar mu ta kasa cimma ruwa.

    \”Ko a satin da ya gabata mun same su domin a biya kudin har sai da muka kara masu wata daya kuma wa\’adin ya kare a wannan satin don haka shi ne dama ta karshe kafin a kulle ofishin\”. Inji Nadada.

     

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here