ZARGIN KISAN KAI: SHEHU SANI YA MAYAR WA DA EL-RUFA\’I MARTANI MAI ZAFI

    0
    676
    Adawa suke da junansu koko dai siyasa ce?

    Daga Usman Nasidi

    HUKUMAR \’yan sanda a jihar Kaduna ta aike da sammaci ga Sanata Shehu Sani domin amsa tambayoyi a kan zargin hannunsa a aikata wani kisan kai.

    Kwamishinan \’yan sanda a jihar, Austin Iwar, ne ya rubuta wasika zuwa ga Sanatan yana mai bukatar sa da ya bayyana a ofishin hukumar na jihar Kaduna nan da ranar 30 ga wata domin amsa tambayoyi.

    \”Muna gayyatar ka dangane da wani laifin kisan kai da hukumar soji, runduna ta 1 da ke nan Kaduna ta aiko mana tare da wani faifan murya na CD da aka ambaci sunanka a matsayin babban wanda ake zargi,\” a cewar Iwar, cikin wasikar da ya aike wa Sanata Shehu Sani.

    Kwamishinan \’yan sandan ya ce aike da wasikar ya zama tilas domin hukumar na son yin adalci a binciken ta.

    An aika wasikar ga Sanata Shehu Sani ta hannun magatakardar majalisar dattijai. Kazalika an aike da kwafi ga shugaban majalisar dattijai, Sanata Bukola Saraki.

    Hakazalika hukumar \’yan sanda bata bayar da cikakken bayani a kan laifin kisan da take zargin hannun Sanatan ciki ba.

    An dade ana tafka rikicin siyasa tsakanin Sanatan na Kaduna ta tsakiya da Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Elrufa’i.

    Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya a majalisan dattawan Najeriya ya mayar da martini mai zafi bayan rahotanni suna nuni da cewa hukumar ‘yan sandan Najeriya ta ambaci sunansa a cikin wadanda ake zargi da laifin kisan kai.

    Hukumar ‘yan sanda ta saki jawabin cewa ana zargin sanatan da hannu cikin wannan harin kisan kai a jihar Kaduna bisa ga wani jawabin kaset da aka ji.

    Kwamishanan ‘yan sandan jihar Kaduna ya rubuta wasikan bukatan ganin sanatan ranan 30 ga watan Afrilu a shelkwatan hukumar na jihar Kaduna domin bayani da bincike.

    Da jin wannan rahoto, Sanatan ya mayar da martini mai zafi inda ya zargi Gwamnan jihar Kaduna da kulla masa sharri. A jawabinsa, Shehu Sani ya ce:

    “Yunkurin da Gwamnan Kaduna Nasiru Elrufai yake yi na kulla mani sharri tare da hannun ‘yan’Sanda ba zai ci nasara ba. Na sami labarin kulle-kulle da yake yi. sharri dan aike ne ko ka tura shi zai dawo maka. ina mai sanar da Nasiru cewa wannan sharrin, kamar na baya da ya yi ba zai hana ni kalubalantar azzalumar gwamnati da yake shugabanci a Jahar Kaduna ba.”

    Rikici tsakani Gwamna Nasir El-Rufa’i da Sanata Shehu Sani ya fara ne tun wani sabani da suka samu a farin gwamnatin APC a 2015. Har yanzu an gaza sulhu tsakaninsu bal rikicin kara zurfafa yake yi

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here