Ya Nemi Musulmi Su Hada Kawunansu Waje Guda

0
709

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

MINISTAN kula da harkokin cikin gida na tarayyar Nijeriya Abdurrahman Bello Danbazau ya yi kira da daukacin Musulmi da su kara hada kansu domin ciyar da kasa gaba.

Danbazau ya yi wannan kiran ne a wajen taron Maulidin sheikh Ibrahim Nyas da aka yi a Kaduna.

Taron dai ya samu halartar dimbin jama\’a Musulmi daga ciki da wajen Nijeriya an kuma yi taron ne da ake yi shekara shekara a filin dandalin Murtala da ke Kaduna.

Danbazau ya ci gaba da cewa hakika hadin kai ne zai tabbatar da zaman lafiya da ci gaban jama\’a baki daya, don haka hadin kai na da matukar amfani.

Danbazau wanda ya wakilci shugaba Muhammadu Buhari a wajen taron ya bayyana cewa shugaban na yi wa dimbin jama\’ar da suka halarci taron fatar alkairi ya kuma bukaci a ci gaba da yi wa kasa addu\’a

A nasa jawabin kakakin majalisar dokokin Jihar Kaduna Alhaji Aminu Abdullahi Shagali, kira ya yi ga daukacin mabiya Shaikh Ibrahim Nyas da su rika yin koyi da halayensa kasancewarsa jagora abin koyi.

Tun kwanaki uku da suka gabata mabiya Shaikh din suka yi ta tururuwa zuwa cikin garin Kaduna domin halartar taron wanda hakan ya sa cikin garin Kaduna ya cika makil da jama\’a maza da mata.

Taron dai ya samu halartar mabiya daga ciki da wajen Nijeriya an kuma yi taro lafiya an tashi lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here