Isah Ahmed, Jos
Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar karamar hukumar Lere da ke jihar Kaduna, Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u ya daukin nauyin yiwa mutane sama da 1000 da suka fama da matsalolin ciwon ido, da ke wannan mazaba magani kyauta.
Shi dai wannan shiri an gudanar da shi ne a babban asibitin garin Saminaka, a karshen makon da ya gabata.
Da yake jawabi a wajen, Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya yabawa dan majalisar kan wannan kokari da ya yi.
Ya ce babu shakka wannan tallafi, zai taimakawa tsofaffi masu fama da matsalolin ciwon ido da ke wannan yanki. Ya ce a irin tsofaffin da suka amfana da wannan shiri, wani ya riga ya cire rai kan zai sake gani a duniya. Sai gashi Allah ya kawo wannan dama.
Sarkin na Saminaka ya yi bayanin cewa irin wadannan tsofaffi suna fitowa a lokutan zabubbuka su yi zabe. Don haka ya yi kira ga ‘yan siyasa zasu rika kirkiro irin wadannan shirye shirye na tallafawa tsofaffi.
A nasa jawabin Dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar karamar hukumar Lere Alhaji Muhammad Lawal Rabi’u ya bayyana cewa sama da mutum 1000 ne aka yiwa maganin matsalolin ciwon ido a wannan shiri da ya dauki nauyin yi, don tallafawa masu larurur ciwon ido da ke wannan yanki.
‘’Wannan shiri ya kunshi duba dukkan masu matsalolin ciwon ido, tare da basu magani da gilashin ido kyauta. Mun yi wannan abu ne domin tallafawa tsofaffi masu larurar ciwon ido a wannan yanki. Kuma mun yi wannan abu ne ganin cewa gwamnati ba zata iya yin komai ba, dole sai jama’a sun taimaka’’.
A nasa jawabin shugaban tawagar likitocin da suka gudanar da wannan aiki, Dokta Kamal ya yabawa dan majalisar kan daukar nauyin wannan shiri, saboda mahimmancin da ido yake da shi ga rayuwar dan adam.
Ya yi kira ga masu hanu da shuni su yi koyi da wannan kokari da wannan dan majalisa ya yi.