\’\’ Ku Rage Kudaden Da Kuke Caji A Asibitocinku\’\’

0
853
A\'iha Buhari ma na yin tallafi ga kiwon lafiya

Rahoton Zubairu Sada

UWARGIDAN shugaban kasa, Hajiya A\’isha Muhammadu Buhari ta nemi asibitoci masu zaman kansu da duba dawainiyar al\’umma da suke zuwa asibitocinsu domin neman magani su rage yawan kudaden da suke cajinsu, tsadar ta yi yawa.

Ta yi wannan kira ne a yayin da ta karbi tawagar kungiyar masu asibitocin kansu a fadar shugaban kasa a Larabar tsakiyar makon nan da muke ciki.

Hajiya A\’isha Buhari ta ce, da yawan \’yan Najeriya da ba su kusa da asibitocin gwamnati suna zuwa asibitocin kudi amma suna haduwa da muguwar tsada a cajin da ake yi masu, kuma wannan ba wai marasa lafiyar yake shafa ba kadai, a\’a har da al\’amuraan kiwon lafiya na kasa baki daya.

Ta ci gaba da cewa, wajibi ne su duba wannan batu sannan su yi sauki da rangwame ga cajin kudaden domin su sami mutanen da za su rika yawan ziyarar asibitocinsu domin samun sauki na kudi da na lafiyarsu.

Shugaban kungiyar dokta Frank Udeton yaba wa Uwargida A\’isha ya yi inda ya ce irin ayyukan da take yi wajen nema wa al\’umma lafiyarsu, musamman mata da yara kanana, lallai za a sami ci gaba a fannin a Najeriya.

Shi kuwa shugaban kungiyar Likitocin Iyalai na duniya, Furofesa Amanda Howe wanda yake a cikin ziyararsa ta aiki Najeriya ta kwanaki biyu, cewa ya yi ayyukan da Uwargida A\’isha take bayarwa abin koyi ne matuka, musamman ma ganin kalubalen da ake shi a bangaren na kiwon lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here