An Kama Mutane 115 A Arangamar ‘Yan Shi’a Da ‘Yan Sanda

0
659
I G Na \'Yan Sandan Najeriya

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

A wata sabuwar arangamar da aka yi a ranar 16/4/2018 a garin Abuja babban birnin tarayyar Nijeriya da aka yi tsakanin jami\’an ‘yan sanda da kuma mabiya shi\’a bangaren Malam Yakubu El- Zakzaky,  rahotanni sun tabbatar da cewa ‘yan sanda sun kama mutane dari da sha biyar.

Bangaren mabiya shi\’a dai sun dade suna zaman dirshan a cikin garin Abuja inda suke ta kiraye-kirayen a saki malaminsu Shaikh Yakubu AL- Zakzaky wanda tun da aka yi waki\’ar birnin Zariya tsakanin sojoji da ‘yan shi\’ar aka kama shi kuma yana hannun jami\’an tsaro.

Kamar yadda rahotannin suka bayyana daga ‘yan sanda sun tabbatar da kama mutane dari da sha biyar kuma suna hannun su, sai dai ‘yan sandan sun gargadi mabiya shi\’ar da su daina tsare tituna lokacin zanga-zangar tasu.

A ta bakin su mabiya shi\’ar sun bayyana cewa suna kan hanyar su ta zuwa ofishin kare hakkin bil\’adama ne sai kawai ‘yan sanda suka fara harba masu barkonon tsohuwa mai sa hawaye daga baya kuma sai ruwan zafi tare da harsashin da suka ce ya jikkata mutanen su da yawa.

\” Mu bukatarmu ita ce a saki malam Zakzaky saboda ba shi da lafiya idanunsa na bukatar a duba shi domin yi masa magani kuma an ce ma sai an je kasashen waje asibiti to me ya sa ake rike da shi bayan mun je kotu an kuma bada hukuncin\”.

Sun kuma ce ko za a karar da su ba za su daina wannan fafutukar a saki jagoransu Yakubu Zakzaky ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here