Mutanen Tudun Wada Sun Yi Jinjina Da Sa Wa El- Rufa\’i Albarka

0
879
Gwamna Malam Nasiru El-Rufa\'i na Jihar Kaduna

Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna

AL’UMMAR unguwar Tudun Wada a cikin garin Kaduna sun jinjina wa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i sakamakon dimbin ayyukan raya kasa da ake aiwatarwa a yankin.

Jama\’ar dai sun shaida wa wata tawagar manema labarai ne da ta ziyarci yankin karkashin jagorancin babban sakatare a ma\’aikatar ayyuka,da gidaje da sufuri Alhaji Muhammadu Murtala Dabo, inda suka shaida wa manema labaran cewa wannan gadar da suka ziyarta an ginata ne tun zamani Sardauna Firimiyan Arewa amma ta karye ba a samu wanda zai gina ta ba sai a yanzu da Gwamna El-Rufa\’i ya kammala aikin baki daya.

\”Wannan gadar a can baya har akan raba aure saboda babu hanyar da za a wuce idan miji da mata na bangare daban-daban shi kenan, amma yanzu kamar an yi ruwa an dauke, Malam Nasiru tuni ya kammala mana ita wanda dalilin hakan mayanka dabbobi ta zama kullum sai san barka muke yi.\” Inji jama\’ar yankin.

Sarkin Fawan Kaduna, Alhaji Suleiman Sabo yabawa tare da jinjina wa Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i ya yi sakamakon wannan namijin kokarin da ya aiwatar na wannan makekiyar gada mai dimbin tarihi da kuma tasiri mai yawa kasancewar ta hanya ce ta mayankar dabbobi.

\”Hakika wannan hanya ta hada dimbin al\’ummar wannan yankin na Tudun Wada da kuma mutanen karamar hukumar Kaduna ta kudu domin suna amfani da ita sosai\”.

Tawagar manema labaran daga cibiyar ‘yan jarida ta kasa (NUJ) sun lashi takobin ganin sun zagaya dukkan wuraren da gwamnatin jihar karkashin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i ta aiwatar da ayyuka a ranar Talata 17/4/2018.

\”Muna murna da cewa wannan aikin an fara shi kuma an kammala shi lafiya, wannan gadar da kuke gani Sardauna ne ya gina ta amma ta karye\”,inji jama\’ar yankin.

Da suke wa manema labaran jawabi mazauna yankin na Tudun Wada kusa da mayankar dabbobi inda aka yi aikin hanya hadu da gadar Danjuma manya-manyan hanyoyin ruwa na zamani masu inganci.

Muhammadu Anas cewa ya yi suna murna ganin irin yadda gwamnatin Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El- Rufa\’i ta tuna da su aka yi masu aiki mai matukar tarihi.

\”Ba mu taba tsammanin cewa za mu samu aiki kamar wannan ba. Aikin nan babba ne domin mun dade muna jira amma sai yanzu kamar budewar idanu har an kammala,kowa na amfanar aikin nan a Kaduna saboda wuri ne mayankar dabbobi ana kai nama ko ina kuma ta wannan hanya ake wucewa, don haka sai godiya da addu\’ar alkairi tsakaninmu da Gwamnan Kaduna Malam Nasiru tare da dukkan mukarrabansa su ci gaba da samun kwarin gwiwar yin aiki ga al’ummomi\”.

Babban sakataren ma\’aikatar ayyuka gidaje da sufuri na Jihar Kaduna Murtala Dabo wanda shi ne idanun manema labaran da suka je wannan aiki mota hudu kowace mota mai cin mutum sha bakwai, cewa ya yi wannan katafaren aikin titin,gada da kuma hanyoyin ruwa mai tsawon mita 375 da mita 100 na hanyoyin ruwa , dukkan su an yi aikin ne a kan kudi Naira Miliyan dari da biyar.

Tawagar manema labaran ta kuma ziyarci wurare irin su Barnawa, Unguwar Rimi, Rafin Guza, Unguwar Sabon Kawo da katafaren titin ‘Yan Majalisu da kuma wurin ajiye manyan motoci na Marabar Jos inda duk naira ke shan kashi ga ayyuka nan a fili ana kan yi kowa na amfana.

Za dai mu ci gaba da kawo maku irin ayyukan da tawagar manema labaran ta gani da kuma tattaunawar da suka yi da babban sakataren.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here