A NIJERIYA  FILATO CE GABA KAN AYYUKAN NOMAN FADAMA-DOKTA HOSEAH ISTIFANUS  

0
704
Mista-Gideon-Dandam-Shugaban-shirin-Fadama-III-a-jihar-Filato.jpg

 Isah  Ahmed, Jos

KWAMISHINAN noma na jihar Filato Dokta Hoseah Istifanus Finangwai ya bayyana cewa jihar Filato ce gaba kan ayyukan Fadama III a Nijeriya. Kwamishinan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi, a wajen taron shugabannin shirin Famada III na jihohin Nijeriya, da aka gudanar a garin Jos.

Ya ce babu shakka shirin Famada III ya sami gagarumar nasara a jihar Filato, sakamakon goyan baya da hadin kan da gwamnatin jihar take bai wa shirin, ta hanyar bayar da kason kudaden da aka dora mata.

Kwamishinan ya yi bayanin cewa  ta hanyar wannan shiri na Fadama III an kafa bankin manoma a jihar, wanda  a duk Nijeriya babu inda manoma suka hadu suka kafa banki sai a wannan jiha.

‘’Kusan duk inda aka shiga a jihar Filato akwai ayyukan da Famada III da aka gudanar. Kuma daruruwan mata da matasa ne suka amfana da ayyukan Fadama III ta hanyar tallafa masu kan noma kayayyakin lambu da kiwon kaji. Ganin cewa a shekara mai zuwa ne, shirin Fadama III zai kare muna son a cigaba da shirin Fadama IIII a Nijeriya’’.

A nasa jawabin shugaban shirin  Famada III a jihar Filato  Mista Gideon Dandam ya bayyana matukar farin cikinsa kan yadda ofishin shirin Fadama III na kasa ya kawo wannan taro jihar Filato.

Ya ce wannan ya nuna cewa an gamsu da irin nasarorin da aka samu kan wannan shiri a jihar Filato.

Ya yi  kira ga dukkan shugabannin shirin Fadama III na jihohin Nijeriya  su cigaba da  tallafawa wajen bunkasa harkokin noma da  inganta rayuwar manoma a Nijeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here