Bullar Zazzabin Lasa A Adamawa: Jama\’a Su Kula Da Muhallinsu -Dakta Fatima

0
726

Saleh Shafi\’u Daga, Yola
KWAMISHINIYAR ma\’aikatar lafiya ta jihar Adamawa Dakta Fatima Atiku Abubakar, ya shawarci jama\’ar jihar, da su kula da muhallin da suke, domin guje wa kamuwa da cututtuka masu yaduwa.
Dakta Fatima ta yi wannan kiran ne lokacin wani taron manema labarai a Yola, ta ce ma\’aikatar ta kara fadada aikinta da samar da ingantattun kayan aiki domin saukake bincike da gano cututtuka masu yaduwa a jihar.
Daukar wadannan matakan sun biyo bayan gano wani mutum guda dauke da kwayar cutar zazzabin bera (Lasa Ferver) a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke Yola FMC, mutumin da hukumomi suka tabbatar da cewa ya mutu.
Ta ce \”kula da tsaftace muhalli da tsaftace kayan abinci kada beraye su taba yana da muhimmanci domin a kauce wa samun bera a gida, kasancewar bera a gida na da hadari ga lafiyar jama\’a\” inji Fatima.
Dakta Fatima Abubakar, ta ce mutumin da aka gano na dauke da zazzabin ya rasu, kuma babu wani da kwayar cutar ta shafa kawo yanzu, ta ce tuni ma\’aikatar ta dauki matakin dakile yaduwar cutar a jihar baki daya.
Ta ce gwamnatin jihar ba ta dauki batun bullar cutar da wasa ba, don haka ta dauki matakin raba kayayyakin bincike, ta bai wa jama\’ar jihar tabbacin cewa babu wani abu da zai faru, domin sun dauki matakan da ya dace.
Ta ce haka kuma ana ci gaba da bincike da killace mutanen da dama da suka yi hulda da mutumin kafin gano cutar, ta ce za a ci gaba da bibiyansu na tsawon kwanaki 21, da dama shi ne adadin kwanakin bayyanar cutar a jikin mai xauke da ita.
Dakta Fatima, ta jaddada bukatar ganin jama\’a sun yi kokarin sanar da hukumomin lafiya duk wani yanayin zazzabin da ba su gane ba, ta ce hanzarta sanarwar zai taimaka wajan gano ko wace irin cuta ce da shawo kan matsalar cikin gaggawa.
Kwamishinar ta gargadi jama\’a da cewa cutar zazzabin Lasa zazzabi ne mai matukar hadari ga rayuwar mutane, ta ce bera abu ne da jama\’a ke tare da shi, wanda kuma yake shiga abinci da ruwa, ta ce \”a kula da tsafta da zuba shara ko\’ina a rika wanke hannu a kowane lokaci\” inji Fatima.
Daga karshe kwamishiniyar ta jajanta wa iyalan mutumin da ya rasa ransa sakamakon kamuwa da cutar, ta ce gwamnatin jihar na duk mai yiwuwa domin hana bullar cutar a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here